2027: Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Man Fetur Ya Samu Gagarumar Goyon Baya

2027: Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Man Fetur Ya Samu Gagarumar Goyon Baya

  • Tsohon shugaban jam'iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya yi kuskure wajen cire tallafin man fetur
  • Nwosu ya yabawa Atiku Abubakar kan alkawarin dawo da tallafin, yana cewa hakan ya nuna jajircewarsa wajen yaye damuwar yan Najeriya
  • Ya ce wasu ma'aikatan gwamnati yanzu suna kwana a tashoshin mota saboda tsadar sufuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar ADC na kasa, Ralph Nwosu, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya yi kuskure wajen cire tallafin man fetur.

Nwosu ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna jajircewa da karfin hali ta hanyar bayyana cewa zai dawo da tallafin man fetur.

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin wata hira a shirin The Morning Show na gidan talabijin na Arise TV.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi wa gwamnoni umarni su inganta rayuwar talaka

Nwosu ya kuma koka kan yadda wasu ma'aikatan gwamnati ke kwana a tashoshin mota saboda rashin iya biyan kudin sufuri da albashinsu.

Nwosu ya soki cire tallafin mai

A cewar tsohon shugaban ADC, idan wata manufa ta gaza, dole ne a amince cewa ta gaza.1

Ya ce manufofin da Atiku da sauran shugabannin ADC ke gabatarwa sun samo asali ne daga tattaunawa mai zurfi da kuma gwaje-gwajen da jam'iyyar ta gudanar.

Ya ce:

“Idan wata manufa ta gaza, to ta gaza. Duk abin da Atiku ko wani shugaban ADC yake fada, abu ne da aka tattauna a kai sosai kuma aka gwada ta hanyoyi daban-daban.
“Haka ake tsara manufofi a cikin al'umma. Jagoranci, kowanne iri ne, ya shafi mutane, ba batun kwalliya ba ne, ba batun injuna ba ne ko wani abu daban. Idan jama'arka ba su da kwarin gwiwa, ba za su iya samar da abin da ake bukata ba.”

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya fito ya fadi gaskiyar dalilin da ya sa yake neman mulkin Najeriya a 2027

'Ma'aikata suna kwana a tashoshin mota'

Nwosu ya ce ADC na da burin gina tattalin arziki mai samar da abubuwa, amma ya jaddada cewa dole ne jama'a su kasance cikin yanayin da zai ba su damar taka rawar gani.

Ya ce binciken da jam'iyyar ke gudanarwa ya nuna yadda tsadar sufuri ke wahalar da ma'aikatan gwamnati, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa:

“Idan ka je tashoshin mota a Najeriya, za ka ga cewa wasu ma'aikatan gwamnati yanzu suna kwana a tashoshin mota saboda, misali, ba za su iya zuwa kullum daga Nyanya ko Karu zuwa tsakiyar Abuja da albashinsu ba.”
Fetur.
Yadda ake hada hadar man fetur a gidan mai Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce idan an tsara manufofi domin jama'a, wajibi ne gwamnati ta rika auna yadda jama'a ke amsa manufofin da kuma irin tasirin da suke yi a rayuwarsu.

Nwosu ya ce tun daga ranar farko ADC ta yi imanin cewa cire tallafin man fetur kuskure ne.

Atiku ya yi alkawarin gyara NELFUND

Kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai sake duba tsarin NELFUND tare da yafe basussukan ilimi ga ɗaliban da suka cancanta.

Atiku ya kuma yi watsi da abin da ya kira ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na amfani da shirin NELFUND a matsayin hujjar cewa ilimi ya zama at sauƙin biya a ƙarƙashin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262