Atiku Ya Kare Kansa daga Sabon Zargin da APC Ta Masa da Neman Hakura da Takara

Atiku Ya Kare Kansa daga Sabon Zargin da APC Ta Masa da Neman Hakura da Takara

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce kotun ICC da ke Paris ba ta same shi da laifin cin hanci da rashawa kan kwangilar wutar Mambilla ba
  • Atiku ya ce bai kasance cikin kwamitin da ya tantance masu neman kwangilar aikin ba, kuma bai bayar da umarnin bai wa kamfanin Sunrise Power aikin ba
  • Martaninsa ya biyo bayan zargin da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ya yi kan wata dala 500,000 da aka tura wa tsohuwar matarsa, Jennifer Douglas, a shekarar 2003

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya musanta zargin cewa ya yi tasiri wajen bayar da kwangilar aikin wutar lantarki ta Mambilla.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban mataimakinsa na musamman kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Juma’a.

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Atiku Abubakar
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa martanin nasa ya biyo bayan hukuncin kotun sasanta rikicin kasuwanci ta ICC da ke Paris, wadda ta yanke hukunci a madadin Najeriya kan takaddamar da kamfanin Sunrise Power ya shigar.

Martanin Atiku ga APC

Atiku ya ce hukuncin kotun ICC bai kunshi wani hukunci da ya same shi da laifin cin hanci ko rashawa ba, yana mai kalubalantar APC da ta nuna inda kotun ta bayyana hakan.

Ya ce bai kasance cikin kwamitin da ya duba tare da tantance shawarwarin kamfanonin da suka nemi aikin ba, sannan bai zauna a kwamitin bayar da kwangilar ba.

Atiku ya bukaci APC ta nuna masa inda kotun ta ce ya karɓi cin hancin dala 500,000 ko kuma ya umarci tsohon Ministan Wutar Lantarki, Olu Agunloye, ya bai wa Sunrise Power kwangilar.

Ya zargi kwamitin yaƙin neman zaɓen APC da sauya abin da ya bayyana a matsayin “zargi” zuwa “tabbataccen laifi”.

Kara karanta wannan

APC ta yi zarge zarge masu nauyi kan Atiku, ta bukaci ya janye daga takara

Batun dala 500,000

A cikin shari’ar, Leno Adesanya, wanda ya kafa Sunrise Power, ya shaida cewa ya tura dala 500,000 ga Jennifer Douglas, tsohuwar matar Atiku, a watan Janairun 2003.

Adesanya ya ce kuɗin wani cinikin canjin kuɗin waje ne da aka gudanar ne saboda Atiku. Sai dai kotun ta ce ba a gabatar mata da isassun takardun da za su tabbatar da wannan bayanin ba.

An tura kuɗin ne a ranar 30 ga Janairu, 2003, ƙasa da wata huɗu kafin a ce an bai wa Sunrise kwangilar gina da gudanar da aikin Mambilla ta hanyar wani kamfani mai suna China Castle Investments.

Atiku Abubakar a gidan shi
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Kotun ta kuma duba matsayin Atiku da irin tasirinsa a gwamnatin tarayya a farkon shekarar 2003, amma Atiku bai kasance ɓangare na shari’ar ba kuma bai bayar da shaida a gaban kotun ba.

Aisha Buhari ta gana da Atiku

A wani labarin, kun ji cewa tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta kai wa Atiku Abubakar ziyara a Abuja, inda tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi bayani.

Kara karanta wannan

Matsayar addinin Musulunci kan sayen hannun jarin matatar Dangote

Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ranar Laraba, yana mai cewa ya ji daɗin ziyarar matar marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin bayanin nasa, Atiku ya kuma yi magana kan matsalar rashin abinci mai gina jiki da yara ke fuskanta a Najeriya, yana mai cewa tsadar rayuwa na barazana ga jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng