Tirkashi: APC Ta Yi Zarge Zarge Masu Nauyi kan Atiku, Ta Bukaci Ya Janye daga Takara
- APC ta zargi Atiku Abubakar da yin abin da ta ce ya jefa Najeriya cikin haɗarin biyan ɗimbin kuɗaɗe kan aikin Mambilla
- Jam’iyyar ta danganta biyan dala 500,000 ga tsohuwar matar Atiku da lokacin da aka bayar da kwangilar aikin Mambilla ga Sunrise Power
- APC ta yi kira ga Atiku da ya janye daga takarar shugaban ƙasa, yayin da yi zarge-zarge masu nauyi kansa kan karbar cin hanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta zargi ɗan takarar shugaban ƙasa na African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, da fifita muradun kansa kan abin da ta bayyana a matsayin muradun ƙasa.
Jam’iyyar ta yi wannan zargin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Dele Alake, ya fitar a Abuja ranar 18 ga Satumba, 2026.

Source: Facebook
Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanya sanarwar a shafinsa na X.
APC ta danganta Atiku da kwangilar Mambilla
APC ta ce sauraron ƙarar da Sunrise Power and Transmission Company Ltd da Leno Adesanya suka shigar kan aikin samar da wutar lantarki na Mambilla da ke jihar Taraba ya bayyana wasu bayanai da ta danganta da Atiku.
Jam’iyyar ta yi iƙirarin cewa Atiku da tsohon Ministan Wutar Lantarki, Olu Agunloye, sun haɗa kai wajen sanya hannu kan wata kwangila da ta ce ba ta samu izini yadda ya kamata ba.
A cewar APC, an sanya hannu kan kwangilar ne a ƙarshen wa’adin farko na mulkin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo, lokacin da Atiku ke matsayin mataimakin shugaban ƙasa.
Jam’iyyar ta ce Obasanjo ya nuna adawa da kuma damuwa kan kwangilar a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya.
Batun Dala 500,000
APC ta kuma danganta kwangilar da wani biyan kuɗi na dala 500,000 da ta ce Leno Adesanya ya aika zuwa wani asusun Citibank na Amurka da ke ƙarƙashin tsohuwar matar Atiku, Jennifer Douglas.
Jam’iyyar ta ce kuɗin an tura shi ne ta wani asusun waje mai suna China Castle Investment, kuma ta yi iƙirarin cewa wasu mu’amalolin kuɗi masu darajar kusan dala miliyan 40 sun bayyana a wani bincike na Majalisar Dattawan Amurka.
APC ta kwatanta lamarin da P&ID
Jam’iyyar ta kwatanta rikicin Mambilla da shari’ar (P&ID), inda wani kamfani ya nemi biliyoyin daloli daga Najeriya kan wata yarjejeniyar aikin iskar gas.
APC ta zargi Atiku da taimakawa abin da ta kira hukumomi ko kamfanoni na cikin gida da ƙasashen waje masu neman cin moriyar Najeriya.
Ta kuma yi iƙirarin cewa Atiku ya guji zuwa Paris domin bayar da shaida a shari’ar, yayin da tsofaffin shugabannin ƙasa Obasanjo da marigayi Muhammadu Buhari suka bayar da shaida domin kare muradun Najeriya.
Jam’iyyar APC ta yi kira ga Atiku ya janye
A ƙarshe, APC ta yi kira ga Atiku da ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027, tana mai cewa batun dala 500,000 da ta danganta da shi kaɗai na iya kasancewa farkon wasu abubuwan da za su fito fili.
Jam’iyyar ta kuma yi kira ga al’ummar jihar Taraba su yi la’akari da rawar da ta ce Atiku ya taka wajen tsaikon aikin tashar wutar lantarki ta Mambilla.

Source: Twitter
Aisha Buhari ta ziyarci Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa matar marigayi Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta kai wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ziyara.
Atiku ya ce ziyarar Aisha Buhari ta kasance mai muhimmanci, yana mai cewa ta tunasar da masu neman shugabanci kan nauyin da ke gabansu na fifita jin daɗin al’umma.
Asali: Legit.ng


