Dan Takarar ADC a Gombe Ya Yi Alkawura, zai Kara da Pantami da Jamilu
- Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar ADC a jihar Gombe, Bala Bello Tinka, ya yi alƙawarin samar da ilimi kyauta tun daga firamare har zuwa matakin jami'a idan ya ci zaɓe
- Alhaji Bala Bello ya kuma alƙawarta janye dokar hana fita da daddare da aka sawa masu sana'ar achaba a da sauran masu hawa babu a jihar Gombe
- Tinka ya bayyana waɗannan alƙawura ne yayin da yake zaga garin Gombe da kewaye domin neman goyon bayan al'umma a ranar Talata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin jam'iyyar ADC, Dr Bala Bello Tinka, ya fara gabatar da tsaren-tsaren da zai gudanar idan har ya lashe zaɓen shekarar 2027.
Tinka ya yi alƙawarin samar da ilimi kyauta tun daga matakin firamare har zuwa jami'a, sannan zai soke takunkumin da aka sawa masu achaba na hana su aiki da daddare.

Kara karanta wannan
Dan takarar gwamna ya sadaukar da albashinsa ga matan mazajensu suka mutu idan ya ci zabe

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa ɗan takarar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga al'umma da magoya bayansa a lokacin yakin neman zaɓe a cikin birnin Gombe da kewaye a ranar Talata.
Tinka zai soke dokar 'yan acaba
A watan Yunir shekarar 2025 ne gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta kakaba dokar hana 'yan achaba gudanar da sana'arsu daga ƙarfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe sakamakon matsalolin tsaro.
Sai dai Tinka ya nuna cewa wannan doka ta shafi dubunnan matasa da sana'ar ta dogara a kansu, dama sauran jama'ar da ke amfani da su, musamman da daddare.
The Sun ta rahoto ya ce:
"Idan aka zaɓe ni gwamna, zan sake duba matakan da aka sakawa 'yan achaba tare da dawo da aiki na tsawon sa'o'i 24, tare da kiyaye duk tsauraran matakan tsaro da suka dace.
"Dubunnan matasa sun dogara da wannan sana'a, kuma mutane da yawa na buƙatar su wajen tafiye-tafiye musamman cikin dare. Ba za mu iya yin watsi da buƙatunsu ba."
Maganar ilimi da lafiya
Bayan haka, Tinka ya yi alƙawarin cewa cikin wata biyu na farko a gwamnatinsa zai cire matsalar fashin waya da ƙwace jaka a tsakanin al'umma, tare da haɗa kai da jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.
Haka zalika game da harkar ilimi da lafiya, ya jaddada cewa ilimi ba na masu kuɗi kaɗai ba ne, don haka zai tabbatar da an samu ilimi kyauta domin 'ya'yan talakawa su samu damar gina makomar su.

Source: Facebook
Tinka ya kuma ƙara da cewa gwamnatinsa za ta samar da kula da lafiya ta kyauta ga mata masu juna biyu tare da magani kyauta ga yara tun daga haihuwa zuwa shekara biyar.
Pantami ya karbi 'yan APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP a jihar Gombe ta karɓi wasu manyan 'yan siyasa da magoya bayansu daga ƙaramar hukumar Yamaltu/Deba waɗanda suka ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki.
Masu sauya sheƙar wadanda suka haɗa da tsofaffin jami'an soja, tsofaffin ma'aikatan gwamnati, da manyan 'yan siyasa sun bayyana goyon bayansu ga PDP gabanin zaɓen 2027.
Tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, da ɗan takarar gwamna na PDP, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ne suka karɓe su a wani ƙayataraccen taro.
Asali: Legit.ng

