Gwamnatin Yobe Ta Yi Magana kan Ba Izala Naira miliyan 300

Gwamnatin Yobe Ta Yi Magana kan Ba Izala Naira miliyan 300

  • Gwamna Mai Mala Buni ya ce alkawarin N300m da aka yi a madadinsa ga JIBWIS gudummawa ce ta kansa, ba ta gwamnatin Yobe ba
  • Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Kabiru Masari, ya yi alkawarin bayar da N300m daga kansa, tare da wasu N300m a madadin Gwamna Buni
  • Gwamnatin Yobe ta ce ba gaskiya ba ne a ce za a biya N600m ɗin daga cikin kuɗaɗen gwamnatin jihar wanda ya jawo cece-kuce a sassan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Yobe – Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa gwamnatinsa ce ta yi alkawarin bayar da N600m ga Jami’ar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS).

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu da gwamnan Yobe sun ba Izalar Jingir Naira miliyan 600

Ya yi karin bayani game da miliyoyin kudin da aka yi alkawarin za a ba wa kungiyar addinin a wani taro da aka yi a jihar Filato a baya-bayan nan.

Gwamnatin jihar ta ce an yi alkawarin ne a matsayin gudummawar kashin kai daga Gwamna Buni da kuma Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Hon. Kabiru Masari.

Gwamnatin Yobe ta wanke kanta daga zargin sa hannu a asusun jama'a
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni Hoto: Mamman Mohammed
Source: Facebook

Wannan karin bayani na kunshe a cikin wata sanarwa da Mamman Mohammed, Daraktan Janar, Yaɗa Labarai da Harkokin Yada Labarai ga Gwamnan Yobe na wallafa a shafinsa na Facebook.

Bayanin gwamnatin Yobe kan JIBWIS

Mamman Mohammed, ya kara da cewa an samu muhawara da rashin fahimta a kafafen sada zumunta kan batun gudummawar.

Ya ce Gwamna Buni, tare da takwarorinsa na Kano, Sokoto, Jigawa, da Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Hon. Kabiru Masari, da wasu manyan baki, sun je Jos ranar Lahadi, 23 ga Agusta 2026, domin halartar wani taron karawa juna sani da JIBWIS ta shirya.

A cewar sanarwar, tawagar ta fara da kai ziyarar girmamawa ga Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, kafin daga bisani ta wuce wurin da aka gudanar da taron.

Kara karanta wannan

'A bar yan Najeriya su yanke hukunci': Bashir Ahmad ya kalubalanci Kwankwaso

Alkawwarin da aka yi wa JIBWIS

A yayin taron, an bai wa manyan baƙin damar gabatar da saƙonnin fatan alheri, inda Gwamna Buni ya gabatar da nasa saƙon, sannan sauran mahalarta suka biyo baya.

Sanarwar ta ce Hon. Kabiru Masari ne na ƙarshe da ya gabatar da saƙonsa, inda a karshen jawabinsa ta bayyana cewa:

“An sanar da ni yanzu cewa JIBWIS na da jami’a da ake ginawa, ina yin gudummawar N300m daga kaina, sannan kuma ina yin alkawarin bayar da wasu N300m a madadin ɗan’uwana, Mai Girma Gwamna Mai Mala Buni.”
Gwamnan Yobe zai bayar da N300m daga aljihunsa ba asusun gwamnati ba
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe Hoto: Mamman Mohammed
Source: Twitter

Sanarwar ta jaddada cewa gudummawar da Masari ya yi a madadin kansa da Gwamna Buni gudummawar kashin kai ce, ba ta gwamnatin Jihar Yobe ba.

“Bugu da ƙari, Hon. Masari ba shi da ikon yin wani alkawari ko ɗaukar wata shawara a madadin gwamnatin Jihar Yobe."

Matsayar Izala game da zaben 2027

A baya, mun kawo labarin cewa kungiyar JIBWIS ta bayyana cikakken goyon bayanta ga matsayar Shugaban Majalisar Malamai ta ƙasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, kan zaben 2027.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah

JIBWIS ta kuma yi kira ga Musulmi da sauran ’yan Najeriya da su shiga harkokin siyasa cikin lumana, gaskiya, adalci da kishin da yan kungiyar suke da shi na tabbatar da kishin kasa.

Ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar ƙarshen taro da ta fitar bayan kammala taron ƙasa kan shiga siyasa da tabbatar da adalci a ranar Lahadi, 23 ga Agusta, 2026, a Jos da ke jihar Filato.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng