Tsohon Shugaban DSS Ya Hango Abin da Zai Faru da Masu Shirin Magudin Zabe a 2027

Tsohon Shugaban DSS Ya Hango Abin da Zai Faru da Masu Shirin Magudin Zabe a 2027

  • Lawal Daura ya ce za a bijire wa duk wani yunƙurin yin magudin zaɓen 2027, yana mai cewa komai ya kamata ya kasance bisa doka da Dokar Zaɓe
  • Daura ya ce masu rajistar zaɓe sun haura miliyan 100, yana mai cewa yaƙin neman ƙuri’u zai fi mayar da hankali kan jawo hankalin masu zaɓe
  • Felix Hyat ya buƙaci matasa su guji zaɓen da ya dogara kawai da addini, ƙabila ko ra’ayin yankin da suka fito

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Lawal Daura, mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na Allied Peoples’ Movement (APM), ya yi magana kan magudin zabe a 2027.

Lawal Daura ya bayyana cewa ba za a bari a lashe zaɓen shekarar 2027 ta hanyar magudin zaɓe ba.

Lawal Daura ya yi magana kan magudin zabe
Dan takarar mataimakin shugaba kasa na APM, Lawal Daura Hoto: Lawal Musa Daura
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce Lawal Daura ya bayyana hakan ne ranar Talata, 6 ga watan Oktoban 2026 wajen ƙaddamar da Kwamitin Gudanar da Yaƙin Neman Zaɓe na Ƙasa (NCMC) na Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta Makinde-Daura (MDPCO).

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban ƙasa ya cika baki, ya ce zai samu ƙuri'u kusan miliyan 70 a zaben 2027

Daura ya yi barazanar bijire wa magudi

Tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ya ce duk wani yunƙurin yin magudin zaɓen 2027 zai fuskanci turjiya.

Ya ce waɗanda ke shirin yin magudi “za su gamu da abin mamaki”.

“Wannan karon, fafatawar gaskiya ce. Ba za mu bar su su nasara da hakan ba. Dole ne mu tabbatar da cewa komai ya gudana bisa doka da kuma Dokar Zaɓe."
“Ga waɗanda suke son yin magudi, suna tunanin za su iya yin dabarar da za ta ba su nasara, to za su gamu da abin mamaki,” in ji Daura.

Masu rajistar zaɓe sun haura miliyan 100

Daura ya ce adadin masu rajistar zaɓe a Najeriya ya haura miliyan 100, yana mai cewa wannan adadi na da muhimmanci matuƙa yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Ya ce jam’iyyun siyasa da ’yan takara suna fuskantar babban aiki wajen neman goyon bayan mafi yawan masu zaɓe.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: INEC ta yi magana kan hukuncin kotu da zai iya shafar takarar su Pantami

A cewarsa, tawagarsa na da burin samun akalla kashi biyu bisa uku na masu rajistar zaɓe miliyan 103.

“Ga mu da muke cikin siyasa, wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci. Abin da ya fi muhimmanci shi ne muna ƙoƙarin neman goyon bayan mafi yawan waɗannan masu zaɓe."
“Tabbas, ba sai wani ya tunatar da mu ba, mun san cewa aiki ne mai matuƙar wahala. Muna da burin samun abin da bai ƙasa da kashi biyu bisa uku na miliyan 103 ba,” in ji shi.

Ya ce ya kamata a nemi ƙuri’a ta hanyar manufofi

Daura ya ce jam’iyyun siyasa da ke neman ƙuri’un ’yan Najeriya ya kamata su mayar da hankali wajen gamsar da masu zaɓe ta hanyar manufofinsu da ingancin ’yan takararsu.

Ya ce bai kamata jam’iyyun su nemi hanyoyin gajarta wa kansu hanya wajen samun nasara ba.

APM na son “sake tsara” Najeriya

Tsohon shugaban na hukumar DSS ya ce manufar jam’iyyarsu ita ce “sake tsara” Najeriya, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Ya ce cimma wannan buri na buƙatar mutane masu inganci, jajircewa, mayar da hankali da kuma ƙudirin yin nasara.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An huro wutar da za ta iya sanya INEC hana Pantami da wasu yin takara a 2027

Lawal Daura ya tabo batun zaben 2027
Gwamna Seyi Makinde tare da Lawal Musa Daura a wajen taron jam'iyyar APM Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Dan takarar shugaban kasa ya cika baki

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na APM, Gwamna Seyi Makinde, ya bayyana cewa jam’iyyarsa na shirin lashe zaben 2027 da gagarumin rinjaye.

Gwamna Makinde ya ce APM na da burin samun aƙalla kashi biyu bisa uku na ƙuri’un masu zaɓe miliyan 103 (kimamin kuri'u miliyan 68).

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng