2027: An Samu Gwamnan APC Na Farko da Ya Nuna Bai Adawa da Tafiyar Wike

2027: An Samu Gwamnan APC Na Farko da Ya Nuna Bai Adawa da Tafiyar Wike

  • Lucky Aiyedatiwa bai ganin akwai laifi a tafiyar da Nyesom Wike ya kirkiro gabanin zaben shekarar 2027
  • Gwamnan ya tabbatar da karfin jam’iyyar APC a jiharsa ta Ondo, ya nuna bai cikin barazanar minista
  • Ministan na Abuja yana tallar Bola Tinubu a sama, amma ya mara wa ‘yan adawa baya a wasu jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Ondo - Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ce jiharsa na nan daram a hannun jam’iyyar APC mai rike da mulkin kasa.

Lucky Aiyedatiwa ya kuma shaida cewa babu wata matsala tsakaninsa da Nyesom Wike, Minista na Babban Birnin Abuja.

Gwamnan Ondo da Nyesom Wike
Gwamnan jihar Ondo da Ministan Abuja, Nyesom Wike Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Source: Facebook

Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya jaddada karfin APC

A hirar da Channels ta yi da shi, ya ce babu abin da ya hada shi da ministan ko tafiyar 'Rainbow Coalition' da yake jagoranta.

Mista Wike ya kirkiro hadin gambizar jam’iyyu daban-daban da ke goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ya samu wa’adi na biyu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga aikin da ba nasa ba, ya fadi abubuwa 3 da suka jawo hatsarin jirgin sojoji

Gwamnan ya ce:

“A jihata, APC ce kawai. Amma hakan ba yana nufin ba ni da alaka da Wike ba. Ba ni da wata matsala da Wike.”

Wike: Gwamnan Ondo ya halatta 'Rainbow Coalition'

Gwamnan ya ce babu laifi a kafa tafiyar Rainbow Coalition, domin siyasa ta ta’allaka ne kan muradu, alaka da hadin gwiwa.

“Idan aka yi magana kan siyasa, tana da alaƙa da muradu, alaƙa da kuma ƙawance.
Don haka, babu wani laifi a samun Rainbow Coalition da Mai Girma Minista Nyesom Wike ke jagoranta.
Babu laifi a kafa kawance ko hadin gwiwa; abin ya danganta ne da muradun wadanda ke son shiga cikinsa”

- in ji shi.

'Rainbow Coalition' jirgin tallar Tinubu ne

The Cable ta ce Aiyedatiwa ya kwatanta kungiyar da sauran kungiyoyin da ke goyon bayan sake zaben Tinubu a shekarar badi.

A lokacin da wasu gwamnonin APC suke yakar shi, gwamnan Ondo ya cewa babu laifi idan manufarta ita ce a yi tallar Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya umarci cafke 'yan 'Tinubu Must Go a Borno'? An ji yadda zancen yake

Ya ce a dokar kasa, kowa yana da yancin shiga kowace kungiya ko hadakar da yake sha'awa.

“Don haka, idan Rainbow Coalition ma kungiyar tallafa wa shugaban kasa ce, mene ne laifin hakan? Babu komai”

- Lucky Aiyedatiwa

Sai dai Aiyedatiwa ya jaddada cewa goyon bayansa ga APC a Ondo bai ci karo da alakarsa da Wike ko kuma ra’ayinsa na siyasa ba.

Gwamnonin APC da suka taso Wike a gaba

An ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana sunayen gwamnonin APC guda uku da ya ce su ne wadanda ke yaki da shi da tafiyarsa.

Gwamnonin jam'iyyar ta APC mai mulki su ne Hope Uzodimma na Imo, AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara da kuma Dapo Abiodun na Ogun.

Ministan ya jaddada cewa tafiyarsa ba tana yaki da jam'iyyar APC ba ne, illa dai tana talla kuma tana goyon bayan sake zaben Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng