Amurka da Saudiyya Sun Turo Muhimmin Sako zuwa Najeriya kan Hatsarin Jirgin Sojojin Sama

Amurka da Saudiyya Sun Turo Muhimmin Sako zuwa Najeriya kan Hatsarin Jirgin Sojojin Sama

  • Kasashen Amurka da Saudiyya sun miƙa ta’aziyyarsu ga Najeriya bayan haɗarin jirgin sojojin sama da ya yi sanadin mutuwar jami’ai da ma’aikatan jirgin 25
  • Jirgin ya yi hatsari ne a garin Igbokoda da ke jihar Ondo yayin da yake kan wata tafiya ta yau da kullum daga Benin City zuwa Legas
  • Shugaban rundunar sojin saman Najeriya ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin hatsarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Najeriya na ci gaba da karbar sakonnin ta'aziyya da taya alhini daga ciki da wajen kasar sakamakon hatsarin jirgin rundunar sojojin sama (NAF), wanda ya auku a jihar Ondo.

Kasashen Amurka da Saudiyya sun miƙa ta’aziyyarsu ga Najeriya bayan wani jirgin saman sojoji ya yi hatsari a Igbokoda, jihar Ondo, ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Ana cikin jimami, ƙasar Turkiyya ta aiko saƙo Najeriya kan hatsarin jirgin sojoji

Trump da Tinubu.
Shugaban Amurka, Donald Trump da takwaransa na Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa dukkan wadanda ke cikin jirgin, wanda ya kunshi fasinjoji 20 da ma’aikatan jirgin biyar da ke cikinsa sun rasu.

Jirgin na kan wata tafiya ta yau da kullum ne daga Benin City zuwa Legas lokacin da ya yi hatsari a Igbokoda, hedikwatar ƙaramar hukumar Ilaje.

Ehimen Ejodame, daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na NAF, ya ce jami’ai 20 da ma’aikatan jirgin biyar ne ke cikin jirgin. Ya ce ba a samu wani da ya tsira ba.

Ya ƙara da cewa Kelvin Aneke, shugaban rundunar sojin saman Najeriya, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin.

Amurka ta yi ta’aziyya

A cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya fitar ranar Talata, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai, abokai da abokan aikin jami’an NAF da suka rasu.

“Muna nan tare da al’ummar Najeriya kuma muna ci gaba da jajircewa wajen ƙarfafa haɗin gwiwarmu ta fuskar tsaro,” in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu bai ji daɗin abin da ya faru da mutane 32 a jirgin saman sojojin Najeriya ba

Saudiyya ta jajantawa Najeriya

A wata sanarwa ta daban, Masarautar Saudiyya ma ta bayyana alhininta ga Najeriya bisa wannan hatsari.

“Masarautar tana bayyana goyon bayanta ga iyalan waɗanda suka rasu, da kuma gwamnatin da al’ummar Najeriya a wannan babban bala’i, tare da yi wa Najeriya da al’ummarta fatan ci gaba da samun tsaro da zaman lafiya,” in ji sanarwar.

A baya, Shugaba Bola Tinubu ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki na ƙasa domin karrama jami’an da suka rasu a hatsarin jirgin sojojin.

Sarki Salman.
Sarkin kasar Saudiyya, Salman Bn Abdul'aziz Al-Saud Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Turkiyya ta jajatawa Najeriya

Kun ji cewa Gwamnatin Turkiyya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga Najeriya kan hatsarin jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) da ya yi sanadin mutuwar mutane.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana ta’aziyyar ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba, 2026.

Ma’aikatar ta ce ta yi matuƙar baƙin ciki kan asarar rayukan da hatsarin jirgin sojin ya haddasa a Jihar Ondo ranar 5 ga Oktoba, 2026, lamarin ya jefa iyalai da dama cikin jimami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262