Muttaqa Darma: Sabon Ministan da Tinubu Ya Nada Ya San Matsayarsa bayan Tantance Shi
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rubuta wasika ga Majalisar dattawa domin neman tantance Muttaqa Rabe Darma a matsayin Minista
- Majalisar dattawan ta tantance Muttaqha Rabe Darma yayin zamanta na ranar Alhamis, 23 ga watan Afirilun 2026
- A lokacin tantance shi, Muttaqa ya bayyana cewa zai yi aiki kafada da kafada da Majalisar dokoki ta kasa don magance matsalar karancin gidaje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta tantance Muttaqa Rabe Darma wanda ya fito daga jihar Katsina a matsayin Minista a tarayyar Najeriya.
Majalisar dattawan ta Najeriya ta tabbatar da Muttaqa Rabe Darma matsayin Minista bayan ta tantance shi da ta yi.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa majalisar ta tabbatar da Muttaqa Rabe Darma ne a yayin zamanta na ranar Alhamis, 23 ga watan Afirilun 2026.
Majalisa ta tabbatar da sabon ministan Tinubu
Tabbatar da Darma ya biyo bayan zaman tantancewa ne, inda aka gudanar da tambayoyi da amsoshi.
Shugaba Bola Tinubu ya rubutawa majalisar dattawa wasiƙa a ranar Laraba, inda ya nemi a tantance tare da tabbatar da Muttaqa Rabe Darma a matsayin Minista.
Sanata Godswill Akpabio, wanda ya karanta saƙon daga Shugaba Tinubu, daga baya ya tura shi zuwa ga kwamitin da ke kula da hakan don ƙarin matakan majalisa, tare da umarnin ba da rahoto da zarar hakan ya yiwu.
Wane aiki sabon ministan zai yi?
Muttaqa Rabe Darma, ya yi alƙawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da majalisar dokoki ta kasa domin magance ƙarancin gidaje a Najeriya.
Ya bayyana tsare-tsare na inganta jagoranci, faɗaɗa hanyoyin samun gidaje masu sauƙin kuɗi, da kuma ƙarfafa ayyukan hukumomi a wannan ɓangaren, tashar Channels tv ta kawo rahoton.
Da yake magana yayin tantance shi a majalisar dattawa, Darma ya ce salonsa zai mayar da hankali ne kan dinke abin da ya siffanta da gibin jagoranci wanda ya kawo cikas ga samar da gidaje masu inganci a faɗin ƙasar.
A cewarsa, haɗin gwiwa da ‘yan majalisa zai kasance mabuɗi wajen kawar da ƙalubalen da aka daɗe ana fuskanta a ɓangaren gidaje.
“Za mu yi aiki tare da majalisar dokoki ta kasa don tabbatar da cewa an magance ƙalubalen gidaje."
- Muttaqa Rabe Darma

Source: Facebook
Muttaqha Rabe Darma ya samo mafita
Ya lura cewa fiye da ‘yan Najeriya miliyan 100 ne matsalar ƙarancin gidaje ta shafa, sannan ya jaddada buƙatar sanya gidaje su kasance masu sauƙin samu da rahusa, musamman ga masu matsakaicin samun kuɗi.
Da yake mayar da martani ga damuwar da Sanata Adams Oshiomhole ya nuna, Darma ya yarda da girman ƙalubalen ƙarancin gidaje a Najeriya, amma ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa za a iya magance shi da ingantattun manufofi da jajircewa.
“Na yi amanna cewa komai mai yiwuwa ne. Zan yi duk abin da zan iya don dinke gibin da ke akwai tare da inganta yanayin."
- Muttaqa Rabe Darma
'Muna masa fatan alheri'
Wani mazaunin Katsina, Abubakar Mika, ya bayyana cewa suna yi wa sabon Ministan fatan alheri a sabon mukamin da ya samu.
"Daya ya tafi daya ya dawo kenan za mu ce a Katsina. Muna yi masa fatan Allah ya taya shi riko, ya kuma ba shi ikon sauke nauyin da aka dora masa."
- Abubakar Mika
Tinubu ya mika bukata wajen majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika sabuwar bukata ga majalisar dattawan Najeriya.
Shugaba Tinubu ya nemi izinin majalisar dattawa domin sake ciyo bashin Dala miliyan 516.3 daga bankin Deutschk da ke kasar Jamus.
Mai girma Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta kinkimo wannan rancen ne domin gina babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


