Duk da Suna Jam'iyya 1, Gwamna Radda Ya Yi Maganar Nadin da Tinubu Ya Yi Masa a Kwamitin Kamfen
- Gwamna Dikko Radda ya yi magana kan nadin da aka yi masa a matsayin daraktan yakin neman zaben Shugaba Tinubu na APC a jiihar Katsina
- Radda ya ce zai hada kan ‘yan APC, shugabannin al’umma, matasa da mata domin samun nasarar Tinubu a zaben 2027
- Gwamnan ya bukaci shugabannin APC da masu ruwa da tsaki a mazabu 361 su kara kaimi wajen karfafa yakin neman zabe tun daga tushe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da nadinsa a matsayin daraktan Jihar Katsina na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.
Nadin na da alaka da yakin neman sake zaben Tinubu a babban zaben 2027, yayin da Radda shi ma ke neman sake zama gwamnan Jihar Katsina.

Kara karanta wannan
Gwamnonin Arewa 6, malaman addini 500 sun bayyana dan takarar shugaban kasarsu a 2027

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Ibrahima Kaulaha Mohammed ya fitar a shafinsa na Facebook, ranar Lahadi, 23 ga watan Agustan 2026.
Radda zai jagoranci kamfen din APC a Katsina
Radda ya tabbatar wa Shugaba Tinubu da shugabannin jam’iyyar APC cewa a shirye yake ya jagoranci yakin neman zabe mai karfi da zai hada kowa a fadin jihar.
Gwamnan ya ce babban abin da zai mayar da hankali a kai shi ne hada kan ‘yan jam’iyya, masu ruwa da tsaki, shugabannin al’umma, matasa, mata da sauran magoya baya a dukkan mazabu 361 na jihar.
Ya ce hakan zai taimaka wajen gina cikakken goyon baya ga Tinubu domin samun nasarar sake zabensa a 2027.
Ya yabawa Tinubu da shugabannin APC
Radda ya nuna godiya ga Shugaba Tinubu da shugabannin jam’iyyar APC na kasa bisa amincewa da shi da suka yi tare da ba shi wannan muhimmiyar damar.
Ya kuma yaba da shigar da wasu ‘yan asalin Katsina cikin Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa, yana mai cewa jihar tana da tarihin samar da mutane masu kwarewa da suka yi fice wajen gudanar da ayyukan jiha da kasa.
Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwar cewa kwarewa da jajircewar ‘yan Katsina da aka nada cikin kwamitin za su kara karfin kokarin APC wajen samun nasarar da ake bukata.
An bukaci a kara karfafa tattaro mutane
Radda ya bukaci mambobin Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa daga Katsina, shugabannin APC da sauran masu ruwa da tsaki a dukkan mazabu 361 da su kara kaimi wajen wayar da kan jama’a da karfafa tsarin jam’iyyar tun daga matakin kasa.
Ya tunatar da cewa Katsina ta nuna karfinta da jajircewarta ga APC a zaben 2023, yana mai cewa akwai bukatar a kara himma a wannan karon.
“Wannan wata dama ce gare mu da za mu kara yin aiki tukuru, mu kasance cikin hadin kai, sannan mu hada kan al’ummarmu domin sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu."
“A shirye muke domin wannan aiki, kuma Jihar Katsina za ta taka cikakkiyar rawa wajen tabbatar da nasarar Shugaban kasa da jam’iyyarmu mai girma.” In ji shi.
Gwamna Radda ya ce APC a Katsina za ta ci gaba da kokarin karfafa hadin kai da tsarin jam’iyyar domin tunkarar zaben 2027.

Source: Facebook
Gwamna Radda ya ba malamai alawus
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta ɗauki malamai addini 7,525 tare da sanya su cikin tsarin karɓar alawus na wata-wata domin yaɗa saƙonnin zaman lafiya, kwanciyar hankali da zaman tare.
Gwamnatin karkashin Gwamna Dikko Radda ta yi haka ne a matsayin wani ɓangare na matakan da ba na yaƙi ba wajen magance matsalar ’yan bindiga da sauran ƙalubalen tsaro.
Asali: Legit.ng

