Gwamna Ya Dauki Zafi da Yan Bindiga Suka Kai Mummunan Hari Masallaci Ana Cikin Sallah

Gwamna Ya Dauki Zafi da Yan Bindiga Suka Kai Mummunan Hari Masallaci Ana Cikin Sallah

  • Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da cewa yan bindiga sun sace masulmai yayin sallar Juma’a a yankin karamar hukumar Borgu
  • Gwamna Mohammed Umaru Bago ya umurci jami’an tsaro su dauki matakan ceto wadanda aka yi garkuwa da su cikin gaggawa
  • Gwamnati ta gargadi jama’a kan yada bayanan da ba a tabbatar da su ba kan lamarin harin da yan bindigar suka kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Gwamnatin Jihar Neja ta yi Allah-wadai kan harin da aka kai kauyukan Gidan-Zana da Kpenya da ke Ƙaramar Hukumar Borgu, inda aka sace mutane yayin sallar Juma’a.

Gwamnatin ta bayyana lamarin a matsayin mummunan hari da ba za a amince da shi ba, wanda ke barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.

Gwamna Bago.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago a taron majalisar zartarwa a Minna Hoto: Umaru Mohammed Bago
Source: Twitter

Yadda aka sace mutane a masallaci

Kara karanta wannan

"Ba sabon alkawari ba"; Abin da Gwamna Radda zai yi kamfen da shi a Katsina

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Obed Nuhu, ya fitar a Minna, kamar yadda Tashar Channels tv ta rahoto.

Gwamnatin ta ce rahotannin farko daga hukumomin tsaro sun nuna cewa wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun mamaye kauyukan a ranar Juma’a, 21 ga Agusta, 2026.

A cewar sanarwar, maharan sun shiga Masallacin Kpenya ne yayin da ake gudanar da sallar Juma’a, inda suka sace mutane da ba a bayyana adadinsu ba, yayin da wasu suka tsere zuwa yankunan da ke kewaye.

Gwamna Bago ya shiga damuwa

Gwamna Mohammed Umaru Bago ya bayyana matuƙar damuwa kan lamarin, tare da umartar hukumomin da abin ya shafa su yi aiki kafada da kafada da jami’an tsaro domin ceto mutanen da aka sace.

Bago ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Neja, yana mai cewa ba za ta sassauta ƙoƙarinta na hana masu aikata laifuka kawo cikas ga zaman lafiyar jihar ba.

Ya ce an tura rundunar haɗin gwiwar jami’an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru domin tantance halin da ake ciki, bin sawun maharan da kuma taimakawa wajen ceto mutanen da aka sace.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara, sun tura yan bindiga da dama lahira

Sai dai gwamnan ya ce saboda yanayin aikin da ake gudanarwa a halin yanzu, ba za a bayyana cikakkun bayanai kan zirga-zirgar jami’an tsaro da wuraren da aka tura su ba.

Mutane nawa aka sace a masallacin Neja?

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa har yanzu ana tantance ainihin adadin mutanen da aka sace da sauran bayanan da suka shafi harin.

Saboda haka, ya buƙaci mazauna yankin da su guji yaɗa rahotannin da ba a tabbatar da su ba, adadin waɗanda aka kashe ko wasu bayanan zato da ka iya ƙara tayar da hankalin jama’a ko kawo cikas ga ayyukan tsaro.

Gwamna Bago.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago yana jawabi bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar MoU Hoto: Umaru Mohammed Bago
Source: Facebook

Gwamna Bago ya yaba da ƙarfin hali da juriyar al’ummar Borgu, tare da tabbatar musu cewa tsaro da lafiyar al’ummar Neja na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sanya a gaba.

An sace mahaifin hakimi a Neja

A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake, Mallam Abubakar Lafiya mai shekaru 90 a duniya a jihar Neja.

An ce Mallam Abubakar Lafiya ba dattijo ne kawai da ke rike da mukamin sarautar gargajiya ba, domin shi ne mahaifin hakimin gundumar Dekara na yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262