Yanzun nan: Masari ya janye daga matsayin abokin takarar Tinubu

Yanzun nan: Masari ya janye daga matsayin abokin takarar Tinubu

  • Alhaji Ibrahim Masari ya janye daga matsayin abokin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a zaben 2023
  • Masari ya tabbatar da batun janyewar nasa a cikin wata takarda da ya saki a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli
  • Mun dai ji cewa Tinubu ya bayyana tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zabe mai zuwa

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Alhaji Ibrahim Masari ya janye daga matsayin abokin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress(APC).

Masari ya tabbatar da hakan ne a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli.

Tinubu da Masari
Yanzun nan: Masari ya janye daga matsayin abokin takarar Tinubu Hoto: APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Nigerian Tribune ta nakalto wasikar na cewa:

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari, Tinubu da Masari sun shiga ganawar sirri a Daura

“Wannan don sanar da shugabannin jam’iyyarmu karkashin jagorancin Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari, mambobin jam’iyyar da kuma mutanen Najeriya, sakamakon tattaunawa mai muhimmanci da na yi da mai rike da tutar jam’iyyar, All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ku tuna cewa na samu alfarma inda aka zabe ni a matsayin abokin takarar Asiwaju Tinubu a watan da ya gabata bayan fafatawar da aka yi a zaben fidda gwanin shugaban kasa gabannin zaben 2023.
“Amma bayan tattaunawa mai zurfi, a yanzu ina burin janyewa. Na fahimci cewa shawarar da na yanke zai ba Asiwaju damar samun karin masauki da hada-hadar da za ta sa jam’iyyar mu ta ci zabe mai zuwa, tare da goyon bayan al’ummar Najeriya.
“Zan janye, na yard azan iya yiwa jam’iyyarmu da kasar hidima a sauran bangarori da dama.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tinubu ya dauki Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa

“Ina burin tabbatar da cewa na gabatar da wasikar janyewa na da takardar rantsuwa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.
"A madadina da na iyali, ina mika godiya ga Asiwaju Tinubu - Shugaban kasa mai jiran gado, Insha Allahu - saboda amince mun da ya yi kuma mun yi alkawarin ci gaba da jajircewa wajen goyon bayansa da jam'iyyar."

Tinubu ya dauki Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa

Mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives (APC) a zaben 2023, Bola Tinubu, ya bayyana abokin takararsa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a babban zaben mai zuwa.

Tinubu ya sanar da hakan ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, a garin Daura, jihar Katsina, yayin da ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari gaisuwar ban girma na babban Sallah, Channels Tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya dauki Musulmi a matsayin abokin takara, CAN ta yi martani

Asali: Legit.ng

Online view pixel