Ba Boye Boye, Gwamna Sule Ya Fadi Jihohi 3 da APC ke Fuskantar Babban Kalubale gabanin 2027
- Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce rikicin cikin gida na APC na daga cikin manyan kalubalen da jam’iyyar ke fuskanta a Arewa ta Tsakiya
- Sule ya bayyana Kwara, Benue da Nasarawa a matsayin jihohin da ake fuskantar irin wannan kalubale, yana mai cewa ana kokarin shawo kan matsalolin
- Gwamnan ya bukaci shugabannin APC su nuna dattako tare da kauce wa kalaman bainar jama’a da za su iya cutar da jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa jam'iyyar APC na fama da rigingimun cikin gida, wanda ya zama babban kalubalen da take fuskanta a Arewa ta Tsakiya gabanin zaben 2027.
Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a wani taron shiyyar Arewa ta Tsakiya da aka gudanar a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) da ke Abuja.

Kara karanta wannan
Siyasa ta ɗauki zafi, 'yan daba dauke da bindigu sun buɗe wa magoya bayan PDP wuta

Source: Facebook
Leadership ta ce taron ya samu halartar shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda; SGF, Sanata George Akume; da kuma Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris.
Sauran jiga-jigan da suka halarta sun kunshi tsohon gwamnan Jihar Kogi, Idris Wada; tsohon gwamnan Jihar Plateau, Simon Lalong; mataimakin gwamnan Jihar Plateau; Sonny ST. Echono da sauran masu ruwa da tsaki daga yankin.
Jihohin da APC ke fama da rikici
Abdullahi Sule ya bayyana Kwara, Benue da Nasarawa a matsayin jihohin da jam’iyyar APC ke fuskantar wannan kalubale, yana mai cewa ana kokarin warware matsalolin.
Ya bukaci a nuna dattako wajen tafiyar da saɓanin, tare da yin kira ga wadanda abin ya shafa da su guji yin kalamai a bainar jama’a da za su iya cutar da jam’iyyar.
Ya ce duk da cewa akwai gagarumin goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu a cikin APC, sabanin da ya shafi ‘yan takara na iya kawo cikas ga kokarin jam’iyyar na samun mafi yawan kuri’u a 2027.

Kara karanta wannan
Ranar yanci: Atiku ya ɗauko batun da yan Najeriya ke buƙata sani kan raba tallafin N75,000
Gwamna Sule ya yi yi gargadi
Sule ya ce:
“Babban kalubalen shi ne wanda ke cikin jam’iyyarmu, akwai mutanen da ke rike da mukamai a cikin APC, amma suna cewa za mu zabi shugaban kasa, ba za mu zabi wannan ba, ba za mu kada wa wancan ba, ba za mu kada muku kuri’a ba.”
Ya ce irin wannan matsaya na iya haifar da bacin rai tsakanin magoya bayan ‘yan takara da shugabannin jam’iyyar suka ki amincewa da su.

Source: Twitter
Gwamnan ya ce:
"Ra’ayina shi ne, ko da abin da irin wadannan mutane ke son yi ke nan, don Allah su rage hayaniyar da suke yi a kai, domin hakan zai shafe mu idan muka ci gaba da yin hayaniya mai yawa tare da nuna isa da alfahari.”
Gwamna Sule ya fadi amfanin cire tallafi
Kun ji cewa gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce jihar yanzu tana karɓar Naira biliyan 14 zuwa 16 a kowane wata, bayan cire tallafin man fetur.
Gwamnan ya ce sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar sun ƙara wa gwamnatocin jihohi kuɗaɗen da za su gudanar da ayyukan raya ƙasa.
Asali: Legit.ng