Tsautsayi Bai Wuce Rana: An Bindige Sarki yayin Jana'izar Wani Basarake

Tsautsayi Bai Wuce Rana: An Bindige Sarki yayin Jana'izar Wani Basarake

  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa an harbe wani basarake a jihar Ondo har lahira yayin jana’izar wani basarake
  • Lamarin ya faru ne ranar Talata yayin da sarakunan gargajiya da al’ummar yankin ke gudanar da jana’izar wani abokin aikinsu da ya rasu
  • ’Yan sandan Ondo sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce an kama wani mutum da ake zargi, sannan aka fara bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ayeka, Ondo - Wani basarake a Ayeka, karamar hukumar Okitipupa ta Jihar Ondo, Cif Akinwalere Akinola ya rasa ransa.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an harbe basaraken ne shi har lahira yayin jana’izar wani sarki dan uwansa a yankin.

An bindige sarki yayin jana'iza basarake
Taswirar jihar Ondo da wasu miyagu suka harbe sarki. Hoto: Legit.
Source: Original

Punch ta ce lamarin ya faru ne ranar Talata, yayin da sarakunan gargajiya da sauran al’ummar yankin ke gudanar da bukukuwan jana’izar abokin aikinsu da ya rasu.

Kara karanta wannan

Lauya ya shiga neman beli da aka maka shugabannin jam’iyyar ADC a kotu

Yan bindiga sun harbe sarki har lahira

Ko a kwanakin baya ma wasu yan bindiga sun kai wani farmaki a jihar Ondo inda suka hallaka wani basarake.

Maharan su shida sun yi garkuwa da Oba Kehinde Jacob Falodun sannan suka kashe shi a kusa da fadarsa da ke a jihar Ondo.

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yi amfani da karfin tuwo wajen fitar da sarkin daga fadarsa kafin su harbe shi.

Rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da faruwar lamarin, sannan ta bayyana matakan da aka dauka zuwa wannan lokaci.

Miyagu sun harbe sarki a Ondo
Sufeta-janar na yan sanda a Najeriya, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Yadda tsautsayin ya fada kan sarki

Wata majiya a yankin ta ce an harba bindiga yayin bikin, inda harsashin ya sami Akinola kai tsaye a kai, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa nan take.

Majiyar, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce, “A yayin shirin, an harba bindiga. Harsashin ya sami Cif Akinwalere kai tsaye a kai, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa nan take.”

Kara karanta wannan

Iyalan sojoji da dukkan dakarun da ke cikin jirgin sojin da ya yi hadari sun mutu

Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin rudani, yayin da har yanzu ba a bayyana yanayin da ya kai ga harbin bindigar ba.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ondo, DSP Abayomi Jimoh, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kama wani mutum da ake zargi da hannu.

Jimoh ya ce an fara bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin da kuma yadda aka yi amfani da bindigar yayin jana’izar, cewar Daily Post.

Kakakin ’yan sandan ya ce:

“An kama wani mutum da ake zargi, a halin yanzu, an fara cikakken bincike.

Gwamna Ondo ya magantu kan hatsarin jirgi

A wani labarin, mun ba ku rahoton cewa Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ce har yanzu ba a gano wani da ya tsira ba bayan wani jirgin sojan sama.

Mutane 32 ne suka kasance cikin jirgin, ciki har da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin bakwai, yayin da jami’ai ke ci gaba da bincike.

Shugaba Bola Tinubu ya yi alhinin mutanen da suka mutu, tare da umartar a gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin wanda ya jawo asarar rayuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.