Ahmed Dangiwa Ya Yi Martani da Tinubu Ya Tsige Shi daga Mukamin Minista

Ahmed Dangiwa Ya Yi Martani da Tinubu Ya Tsige Shi daga Mukamin Minista

  • Tsohon ministan gidaje da raya brane, Ahmed Dangiwa, ya miƙa godiyarsa ga Shugaba Bola Tinubu bisa damar da ya ba shi na yi wa ƙasa hidima
  • Dangiwa ya bayyana cewa ya yi amfani da lokacinsa a matsayin minista wajen bayar da gudunmawar tabbatar da nasarar "Renewed Hope Agenda"
  • Yayin da yake shirin miƙa ragama, tsohon ministan ya lissafa wasu daga cikin manyan nasarorin da ya samu a shekara daya da ya yi kan kujerar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ya fito ya yi martani, jim kadan bayan an sanar da tsige shi daga mukamin ministan gidaje da raya birane.

Dangiwa ya nuna tsantsar godiyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa damar da ya ba shi na zama ɗaya daga cikin mambobin majalisar zartarwa ta tarayya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada sababbin ministoci 2 da ya fatattaki Wale Edun da Ahmed Dangiwa

Ahmed Dangiwa ya yi ruwan godiya ga Tinubu duk da an tsige shi daga minista
Tsohon ministan gidaje da raya birane, Arc. Ahmed Dangiwa yana jawabi a Abuja. Hoto: @Arch_Dangiwa
Source: Twitter

Martanin Dangiwa bayan tsige shi daga minista

Tsohon ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai tallafa masa kan yaɗa labarai, Mark Chieshe ya fitar, kuma MS Ingawa ya wallafa a shafinsa na X.

A cikin sanarwar, Dangiwa ya ce yin aiki a ƙarƙashin Tinubu babbar daraja ce a gare shi, yana mai jaddada cewa ya yi farin cikin yadda aka amince da shi domin ya jagoranci sauye-sauye a fannin gidaje na Najeriya.

Outgoing Minister Dangiwa ya bayyana cewa a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, ma'aikatar ta samu nasarori masu gari wajen maida fannin gidaje ya zama ginshiƙin bunƙasar tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi.

Nasarorin Dangiwa a matsayin minista

Ya bayyana wasu daga cikin manyan nasarorin nasa da suka haɗa da:

  • Ƙaddamar da shirin gina gidajen "Renewed Hope" don samar da muhalli ga marasa karfi.
  • Ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu wajen gina gidaje.
  • Gudanar da gyare-gyare a fannin sarrafa filaye da kuma tsarin samar da kuɗaɗen gina gidaje.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Shugaba Tinubu ya runtuma kora, ya fatattaki wasu ministoci 2

Sanarwar ta ce:

"Ministan mai barin gado ya nuna cewa a karkashin jagorancin Shugaba Tinubu, ma'aikatar ta samu manyan nasarori a daidaita fannin gidaje, wanda ya samar da bunkasa tattalin arziki, samar da ayyuka da ci gaban kasa."
Dangiwa ya godewa Tinubu da ya ba shi damar kasance wa a majalisar zartarwa ta tarayya.
Shugaba Bola Tinubu na jagorantar zaman majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja. Hoto: @PBATMediaCentre
Source: Twitter

Dangiwa zai mika ragamar shugabanci

Dangiwa ya kuma gode wa mambobin majalisar zartarwa, abokan aikinsa, da ma'aikatan ma'aikatar gidaje bisa goyon bayan da suka ba shi.

Ya bayyana cewa tare suka samar da ginshiƙi mai ƙarfi na yadda za a ci gaba da gina gidaje masu ɗorewa a Najeriya, kamar yadda aka wallafa a shafin ma'aikatar na intanet.

Yayin da yake bayar da tabbacin cewa zai miƙa ragamar shugabanci cikin tsari kamar yadda shugaban ƙasa ya umarta, ya kuma yi wa sabon jagoran da zai zo, Malam Muttaqa Rabe Darma, fatan alheri.

Tinubu ya nada sababbin ministoci

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya yi garambawul a majalisar zartarwa ta tarayya ta hanyar sallamar ministoci biyu, Wale Edun, da Ahmrd Dangiwa.

Kara karanta wannan

"Najeriya ta yi rashi," Tinubu ya yi magana mai ratsa zuciya da Galadima ya mutu

Taiwo Oyedele ne zai karɓi ragamar ma'aikatar kuɗi, yayin da aka naɗa Muttaqha Rabe Darma (PhD) domin ya jagoranci ma'aikatar gidaje da birane.

An umarci tsohon ministan ma'aikatar, Ahmed Dangiwa, da ya mika ragamar ma'aikatar ga Karamin Ministan da ke karkashinsa yayin da ake jiran kammala tantance Muttaqa Darma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com