An Kai Karar TikTok Kotu kan Zargin Hana Wasu Jihohin Arewa Amfani da Manhajar
- Kungiyar Digital Justice ta kai TikTok ƙara a Babbar Kotun Tarayya kan zargin takaita masu amfani da manhajar a wasu jihohin Arewa
- Ta ce takunkumin da aka sanya a Kaduna, Kebbi, Kano da Sokoto ya tauye ’yancin fadin albarkacin baki tare da nuna bambanci
- Ta bukaci kotu ta umarci TikTok ta cire takunkumin, ta daina sake sanya shi, sannan ta wallafa uzuri a jaridu uku na kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kungiyar Digital Justice and Sustainable Development ta shigar da TikTok ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Kungiyar tana zargin TikTok da takaita masu amfani da manhajar musamman a wasu jihohin Arewa da ta ce tauye hakkinsu ne.

Source: Getty Images
A ƙarar, wacce Daily Trust ta gani, ƙungiyar ta zargi TikTok da hana ko takaita masu amfani da manhajar a Kaduna, Kebbi, Kano da Sokoto.
Abin da kungiyar ke bukata daga kotu
Ta hannun lauyanta, Festus Ogun, ƙungiyar ta roƙi kotu ta tantance ko takunkumin ya tauye ’yancin fadin albarkacin baki da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Ƙungiyar ta kuma bukaci kotu ta tantance ko bambancin da ake yi wa masu amfani da TikTok a jihohin ya zama nuna bambanci.
An shigar da ƙarar ne ranar 5 ga Oktoba, 2026, bisa sashe na 39, 42, 45 da 46 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
Haka kuma, ƙarar ta dogara da Dokokin Kare Hakkokin Ɗan Adam na shekarar 2009 da wasu tanade-tanaden Yarjejeniyar Afirka kan Hakkokin Ɗan Adam.
Mai ƙarar ya ce TikTok ba ta da ikon doka na takaita masu amfani a jihohin Arewa, yayin da sauran sassan ƙasar ke samun damar amfani da manhajar.
Ƙungiyar ta roƙi kotu ta ayyana takunkumin a matsayin “ba daidai ba, ya saba wa kundin tsarin mulki kuma ba bisa ka’ida ba”.
Ta ce matakin ya take muhimmiyar ’yancin fadin albarkacin baki da kuma ’yancin samun kariya daga nuna bambanci ga masu amfani da manhajar.
Ƙungiyar ta kuma bukaci kotu ta umarci TikTok ta cire takunkumin nan take, tare da hana kamfanin sake takaita masu amfani a Arewacin Najeriya.
Haka kuma, ta nemi kotu ta hana TikTok takaita masu amfani a kowace irin jiha a ƙasar ba tare da ingantaccen dalilin doka ba.
Bugu da ƙari, ƙungiyar ta bukaci kotu ta umarci TikTok ta wallafa uzurin jama’a a jaridu uku na ƙasa kan zargin take hakkokinta.

Source: Getty Images
Rokon kungiyar ga kotu game da TikTok
Kungiyar ta roƙi kotu ta tantance ko takunkumin geoblocking ya saba wa sashe na 39 na kundin tsarin mulki, wanda ke kare ’yancin fadin albarkacin baki.
Ta kuma bukaci a tantance ko bambancin mu’amala da masu amfani a sassan Najeriya ya saba wa sashe na 42 na kundin tsarin mulki.
Sashe na 42 ya haramta nuna bambanci, yayin da Mataki na 2 na Yarjejeniyar Afirka kan Hakkokin Ɗan Adam shi ma ya tanadi irin wannan kariya.
An shigar da ƙarar a sashen Abuja na Babbar Kotun Tarayya, inda aka sanya TikTok Inc., mai adireshi a Culver City, California, Amurka, a matsayin wanda ake ƙara.
Kotun ta umurci TikTok da ta shigar da bayyanan kare kanta cikin kwanaki biyar bayan an mika mata sammaci.
Ta ce idan kamfanin bai bayyana a gaban kotun cikin wa’adin ba, za ta iya bayar da duk wani umarni da ta ga ya dace.
An gurfanar da yar TikTok a kotu
A baya, an ji cewa kotu ta ba da umarnin a tsare Khadija Muhammad Yar Lele a gidan gyaran hali da ke Kano kan zargin bata sunan wani dan siyasa da kuma zaginsa.
Bayanai sun nuna cewa an gurfanar da matashiyar, wacce ta dhahara a TikTok a gaban babbar kotun Shari’a da ke Post Office, Kano Municipal.
Kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa 14 ga Oktoba, 2026 bayan sauraron kowane bangare a zaman da ta yi.
Asali: Legit.ng


