Rigimar Dangote da Masu Shigo da Fetur Najeriya Ta Dauki Sabon Salo

Rigimar Dangote da Masu Shigo da Fetur Najeriya Ta Dauki Sabon Salo

  • Matatar Dangote ta daina sayar da fetur ga ’yan kasuwar da ke shigo da mai, tana zargin suna haɗa kayanta da man da ba a tabbatar da ingancinsa ba
  • Wasu ’yan kasuwa sun koma kotu domin neman a ci gaba da ba su lasisin shigo da fetur, saboda fargabar ƙarancin mai
  • ’Yan kasuwar sun zargi Dangote da ƙoƙarin hana shigo da fetur, tare da ƙalubalantar matatar ta gabatar da hujjar rashin ingancin man da ake shigowa da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Matatar Man Fetur ta Dangote ta dakatar da sayar da Premium Motor Spirit (PMS), wato fetur, ga manyan ’yan kasuwar da ke shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

Wani jami’in matatar ya tabbatar da hakan, inda ya ce matatar ba za ta ƙara sayar da fetur ga ’yan kasuwar da ke haɗa man Dangote da man da ake shigowa da shi ba.

Kara karanta wannan

Hukumar NRS mai karbar haraji na daukar ma'aikata? An ji bayanin gaskiya

Matatar Dangote na rigima da masu shigo da mai
Hamshakin attajiri, Aliko Dangote Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jami'in matatar ta Dangote da ke jihar Legas wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da hakan ne ga jaridar The Punch.

Dangote ya zargi ’yan kasuwa da haɗa man fetur

Jami’in ya ce matatar ta ɗauki matakin ne saboda wasu ’yan kasuwa na haɗa fetur ɗin da ta samar da man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje.

“Ba ma sayar da fetur ga waɗanda ke shigo da mai, domin suna ƙoƙarin haɗa kayayyakinmu masu inganci da kayayyakin da suke shigowa da su masu ƙarancin inganci,” in ji jami’in.

Wani jami’in daban ya bayyana cewa yanzu matatar ta fi son sayar da fetur ga ’yan kasuwar da ba sa shigo da mai, musamman mambobin Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN).

“Mun fi sayar da fetur ga ’yan kasuwa masu zaman kansu da sauran waɗanda ba sa shigo da mai,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Rigima sabuwa: An sake kai hari mai zafi a Saudiyya

Dalilin da ya sa wasu ’yan kasuwa suka garzaya kotu

An fahimci cewa wannan mataki ne ya sa wasu ’yan kasuwar mai suka garzaya kotu domin neman umarnin da zai tilasta wa Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA) ci gaba da ba su lasisin shigo da fetur.

’Yan kasuwar na fargabar cewa za su iya shiga matsala idan aka hana su shigo da fetur a lokacin da matatar Dangote ta dakatar da sayar musu da mai.

Tun da farko, matatar Dangote ta yi barazanar dakatar da harkokin kasuwanci da ’yan kasuwar da ke shigo da fetur, tana zarginsu da haɗa man fetur ɗinta mai darajar Euro-5 da man da ake shigowa da shi.

Matatar ta ce wannan al’amari na iya haifar da matsalar tantance bambancin da ke tsakanin man da ita kanta ta samar da kuma wanda wasu ɓangarori suka haɗa ko sarrafa daga baya.

’Yan kasuwar mai sun yi tir da matakin

Sai dai masu shigo da mai da wasu ’yan kasuwar man fetur sun yi tir da matakin Dangote na hana sayar da fetur ga ’yan kasuwar da ke shigo da mai.

Kara karanta wannan

Mara lafiya ya mutu bayan tare motar asibiti don motocin babban minista su wuce

'Yan kasuwar sun bayyana matakin a matsayin yunƙurin hana shigo da fetur cikin Najeriya.

Dangote ya daina sayar da fetur ga masu shigo da mai
Aliko Dangote na jawabi a wajen taro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dangote ya yi rangwame ga dalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar da shirin tallafin hannayen jai na matatar Dangote ga Dalibai a Najeriya.

Shirin zai bai wa daliban Najeriya masu shekaru 18 zuwa sama karin hannayen jari 10 na matatar Dangote kyauta, bayan sun sayi akalla hannayen jari 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng