Mayakan Houthi Sun Farmaki Filayen Jiragen Sama 2 a Saudiyya

Mayakan Houthi Sun Farmaki Filayen Jiragen Sama 2 a Saudiyya

  • Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Saudiyya ta ce hare-hare kan filayen jiragen sama na Jazan da Najran sun jikkata mutane uku
  • Houthi sun ce sun kai hari kan wurare da dama a Kudancin Saudiyya, ciki har da filayen jiragen sama da sansanonin soji
  • Gwamnatin Yemen ta ce dakarunta sun kwace Mocha da wasu muhimman wurare kusa da mashigar Bab al-Mandeb, amma Houthi sun musanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Riyadh, Saudiyya - Akalla mutane uku sun jikkata bayan hare-hare kan filayen jiragen sama na Jazan da Najran da ke kusa da iyakar Saudiyya da Yemen.

An kai hare-haren ne yayin da fada tsakanin Saudiyya da mayakan Houthi ke ƙara tsananta a kasar Yemen.

Houthi ta kai hari Saudiyya
Wani wuri na ci da wuta bayan kai hari a Saudiyya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta ce Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya ce ta tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, 6 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun tare babbar hanya a Zamfara, an yi awon gaba da matafiya

Mutane uku sun samu raunuka

Hukumar ta ce hare-haren sun haddasa raunuka marasa tsanani ga mutane uku, tare da lalata wasu kadarori.

“Hare-haren sun haddasa raunuka marasa tsanani ga mutane uku da kuma lalacewar kadarori,” in ji cikin sanarwar.

Houthi sun ce sun kai hare-hare a Kudancin Saudiyya

Mayakan Houthi, wata ƙungiyar masu ɗauke da makamai da aka fi sani da Ansar Allah, sun ce a daren Litinin dakarunsu sun kai hari kan wurare daban-daban a Kudancin Saudiyya.

Sun ce cikin wuraren da suka kai wa hari akwai filayen jiragen sama da kuma wuraren da sojojin Saudiyya suke.

Sai dai hukumomin Saudiyya ba su bayyana cikakken bayani kan hare-haren ba, yayin da ake ci gaba da faɗa tsakanin ɓangarorin.

Gwamnatin Yemen ta ce ta kwace Mocha

A ranar Litinin, gwamnatin Yemen da duniya ta amince da ita ta ce dakarunta sun sake kwace ikon birnin tashar jiragen ruwa na Mocha.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Sabon rikici ya barke a Neja, an samu asarar rayuka

Gwamnatin ta kuma ce dakarunta sun karɓe wasu muhimman wurare kusa da mashigar Bab al-Mandeb, yayin da take ci gaba da wani babban farmaki kan Houthi.

Sojojin gwamnatin Yemen da Saudiyya ke mara wa baya sun kuma ce an fara wani “babban farmaki” kan Sana’a, babban birnin Yemen da Houthi ke iko da shi tun shekarar 2014.

Sai dai Houthi sun musanta cewa an kwace Mocha. Har yanzu ba a samu damar tabbatar da ikirarin da ɓangarorin ke yi daga fagen daga ba.

Ƙawancen Saudiyya ya fara kai hare-haren sama

A ranar Litinin, 5 ga watan Oktoban 2026, ƙawancen sojin da Saudiyya ke jagoranta wanda ke mara wa gwamnatin Yemen baya shi ma ya ce ya fara wani samame na sama kan Houthi.

Mai magana da yawun ƙawancen, Manjo-Janar Turki al-Maliki, ya ce jiragen yaƙi 100 na taimaka wa dakarun gwamnatin Yemen.

Ya kuma ce ƙawancen ya samar da “kariyar sararin samaniya” a yankin Bab al-Mandeb. A cewarsa, an lalata ɗaruruwan wuraren Houthi a hare-haren.

An kai hare-hare a Saudiyya
Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Houthi ta kai hari Saudiyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Houthi ta Yemen ta yi ikirarin cewa ta kai hari kan wata babbar cibiyar man fetur a Saudiyya.

Kungiyar Houthi ta ce ta kai harin ne da makamai masu linzami masu cin dogon zango da jirage marasa matuƙa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng