Da Gaske Tinubu ba Shi da Lafiya? Shugaban Kasa Ya Yi Magana

Da Gaske Tinubu ba Shi da Lafiya? Shugaban Kasa Ya Yi Magana

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa game da lafiyarsa bayan komawarsa Najeriya daga hutun aiki a Turai
  • Tinubu ya ce babu wata matsala da ke damunsa, yana mai bayyana kansa a matsayin mai lafiya kuma a shirye yake ya ci gaba da aiki
  • Shugaban ya dawo Najeriya ne ranar Talata bayan shafe kusan mako huɗu a Turai, inda ya fara zama a Landan kafin ya koma Paris a Faransa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da damuwar da wasu ke nunawa game da lafiyarsa, yana mai cewa yana cikin koshin lafiya kuma a shirye yake ya ci gaba da aiki bayan dawowarsa Najeriya daga Turai.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata bayan ya isa Legas daga Paris ta Faransa, inda ya shafe wani bangare na hutun aikinsa na tsawon mako huɗu.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi magana kan El Rufa'i da yadda ake zalunci a Najeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a wajen taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa bidiyon Bola Tinubu a Facebook a lokacin da ya isa jihar Legas.

Maganar Tinubu kan lafiyarsa

Da aka tambaye shi game da damuwar da wasu ’yan Najeriya da magoya bayansa suka nuna kan lafiyarsa a ƙarshen hutunsa, Tinubu ya ce babu wata matsala da ke tattare da shi.

Ya ce:

“A shirye nake in yi aiki, a shirye nake in yi jagoranci. Babu wata matsala.
“Jita-jita za ta ci gaba da fitowa daga siyasa, amma gaskiyar magana ita ce ina nan kalau. Ina cikin koshin lafiya kuma a shirye nake.”

Yadda Tinubu ya shafe hutunsa

Tinubu ya bar Najeriya ranar 30 ga Agusta domin fara hutun aiki na tsawon mako uku a Turai, inda ya fara zama a Landan kafin ya zarce Paris ta Faransa.

Fadar shugaban ƙasar daga baya ta sanar da ƙara tsawon zamansa a Turai, tana mai cewa yana ci gaba da bibiyar abubuwan da ke faruwa a Najeriya tare da jagorantar harkokin gwamnati daga can.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin Shugaba Tinubu na kwance ba shi da lafiya a ƙasar waje

Punch ta wallafa cewa A Paris, Tinubu ya gana da Shugaban Faransa Emmanuel Macron a wani liyafar cin abinci ta sirri, sannan ya gana da ’yan kasuwa ciki har da Vincent Bolloré na Bolloré Group.

Shugaban Najeriya da na Faransa
Shugaba Bola Tinubu da Emmanuel Macron. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A ranar Litinin kuma ya gana da shugaban First HoldCo, Femi Otedola. Haka kuma, a makon da ya gabata, ya halarci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin Ogun da DP World.

Zargin da Sowore ya yi

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu yana kwance a wani asibiti a Faransa.

Sowore ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira, inda ya danganta kalamansa da tsawon lokacin da Tinubu ya shafe ba ya Najeriya bayan fara hutun da aka sanar cewa zai ɗauki mako uku.

Sowore ya kuma yi zargin cewa shirya fitowar Tinubu gaban jama'a su domin ɓoye wata matsalar lafiya mai tsanani, tare da kwatanta lamarin da abubuwan da suka faru a gwamnatocin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng