Ba Sassauci: Yadda Dakarun Sojoji Suka Hallaka 'Yan Ta'adda 52
Hedikwatar Tsaro ta ce an samu hare-hare 367 a wuraren da sojoji ke gudanar da ayyuka daban-daban a Najeriya cikin watan Satumba 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Operation Enduring Peace ce ta fi fuskantar hare-hare da 147, sai Fansan Yamma da 115, yayin da Whirl Stroke ta samu 55
Sojoji sun ce sun kama ’yan ta’adda da masu aikata laifuffuka 350, sun ceto fararen hula 655 da aka yi garkuwa da su, sannan ’yan tawaye 75 sun mika wuya
FCT, Abuja - Hedikwatar Tsaron Najeriya ta ce an samu hare-hare 367 a wurare daban-daban da rundunar soji ke gudanar da ayyuka a fadin ƙasar cikin watan Satumba 2026.
Bayanan da hedikwatar ta fitar sun nuna cewa Operation Enduring Peace ce ta fi kai hare-haren, inda aka samu 147. Sai Operation Fansan Yamma da hare-hare 115, yayin da Operation Whirl Stroke ta samu 55.

Source: Twitter
Haka kuma, Operation Hadin Kai ta kai hare-hare 33, Operation Savannah Shield ta samu 13, sannan Operation Udo Ka ta samu hudu. A gefe guda, Operation Delta Safe ba ta samu rahoton wani hari ba a cikin lokacin, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu saboda cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yanci
Sojoji sun ce sun dakile hare-haren
Daraktan Ayyukan Yaɗa Labaran Tsaro, Maj.-Gen. Michael Onoja, ya bayyana hakan ya bayyana hakan yayin da yake magana kan nasarorin da sojoji suka samu ranar Laraba, 30 ga watan Satumban 2026, TheCable ta kawo labarin.
Ya ce sojojin sun gaggauta tunkarar maharan ta hanyar amfani da ƙwarewar yaƙi, makamai masu ƙarfi da dabarun aikin soji, inda suka yi nasarar dakile hare-haren.
An kama ’yan ta’adda da masu aikata laifuka 350
Onoja ya ce dakarun sun kuma kama ’yan ta’adda da masu aikata laifuka 350 a cikin watan. Ya ƙara da cewa an ceto fararen hula 655 da aka yi garkuwa da su, yayin da ’yan tawaye 75 suka miƙa wuya ga jami’an tsaro.
A cewarsa, sojojin sun kuma kashe ko dakile ’yan ta’adda da masu aikata laifuka 52 a yayin ayyukan.
An kwato makamai da harsasai
Daraktan ya ce sojojin sun kwato makamai 52 da kuma harsasai 2,335 a lokacin ayyukan.
Haka kuma, sun tarwatsa wuraren tace man fetur ba bisa ƙa’ida ba guda takwas, tare da kwato sama da lita 304,822 na man fetur da aka sace.
Hedikwatar Tsaro ta ce za ta ci gaba da ayyuka
Onoja ya ce sakamakon ayyukan da sojoji suka samu a watan Satumba ya nuna ƙudurin Rundunar Sojin Najeriya (AFN) na ci gaba da aiki a dukkan wuraren da ake gudanar da ayyukan soji domin samar da ingantaccen tsaro a ƙasar.
“Bayanan ayyukan watan Satumba sun nuna ƙudurin AFN a dukkan wuraren ayyukan soji na tabbatar da samar da yanayi mai aminci da tsaro a ƙasar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa dakarun sun dakile ’yan ta’adda da masu aikata laifuka 52, sun kama 350, sun ceto fararen hula 655 da aka yi garkuwa da su, yayin da ’yan tawaye 75 suka miƙa wuya.
Ya ce an kuma kwato makamai 52 da harsasai 2,335, an tarwatsa wuraren tace man fetur ba bisa ƙa’ida ba guda takwas, tare da kwato sama da lita 304,822 na man fetur da aka sace.

Source: Twitter
An kaddamar da bataliyoyin sojoji a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta kaddamar da sababbin bataliyoyin sojoji uku a jihar Zamfara.
Rundunar sojojin ta kaddamar da bataliyoyin ne domin ƙarfafa ayyukan tsaro da inganta gaggawar mayar da martani ga barazanar tsaro.
Asali: Legit.ng

