Bayan Faduwar APC a Osun, Tinubu Ya Tura Muhimmin Sako ga Ademola Adeleke
- Shugaba Bola Tinubu ya yi martani bayan nasarar zaben Gwamnan Osun, Ademola Adeleke da aka yi l
- Tinubu ya bukaci Adeleke ya haɗa kan al’ummar Osun ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyunsu ba
- Shugaban ƙasar ya yaba wa sauran ’yan takara, INEC da jami’an tsaro saboda gudunmawar da suka bayar wajen gudanar da zaɓen lumana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan Osun da aka yi a jiya Asabar.
Tinubu ya taya Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, murnar lashe zaɓen gwamnan jihar yana mai cewa nasarar ta tabbatar da amincewar al’ummar jihar gare shi.

Source: Facebook
Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa ta bakin hadiminsa, Bayo Onanuga da aka wallafa a shafin X a yau Lahadi 16 ga watan Agustan 2026.
Shugaban ya ce ya kira Adeleke a yau Lahadi domin taya shi murnar nasarar da ya samu a zaɓen.
Tinubu ya ce sake zaɓar Adeleke wata alama ce da ke nuna cewa dimokuraɗiyya za ta ci gaba da bunƙasa a Najeriya ƙarƙashin mulkin jam’iyyar APC.
Tinubu ya kuma yi fatan Adeleke zai samu nasara yayin da yake shirin jagorantar Osun na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.
Ya bukaci sabon zaɓaɓɓen gwamnan da ya mayar da hankali wajen haɗa kan al’ummar Osun tare da ƙarfafa su wajen cimma ci gaba, zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki da zamantakewa.
Shugaban ƙasar ya ce bai kamata bambancin zaɓin siyasa da jama’a suka yi a lokacin zaɓen ya zama abin raba kan al’ummar jihar ba.
A cewarsa, Adeleke na da nauyin haɗa kan dukkan al’ummar jihar tare da yi musu jagora zuwa ga samun ci gaba da kwanciyar hankali.
Tinubu ya kuma yaba wa sauran ’yan takarar da suka fafata a zaɓen, yana mai cewa ƙarfin hali da ɗa’a da suka nuna sun taimaka wajen zurfafa al’adun dimokuraɗiyyar Najeriya.
Ya ce sakamakon zaɓen ya nuna ra’ayin al’ummar Osun, yana mai bayyana hakan a matsayin tabbacin cewa dimokuraɗiyya za ta ci gaba da bunƙasa a Najeriya.
Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da jami’an tsaro bisa gudanar da zaɓen cikin lumana da gaskiya, wanda ya samar da wanda ya yi nasara a fili.
Kwankwaso ya taya Adeleke murnar lashe zabe
An ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi martani ga Gwamna Ademola Adeleke bayan ya sake lashe zaɓen gwamnan Osun da aka gudanar.
Kwankwaso ya yaba wa al’ummar Osun saboda amfani da haƙƙinsu na zaɓe, yana mai cewa sakamakon ya nuna ƙarfin ikon jama’a.
Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC ya kuma yaba wa INEC, tare da kira ga masu ruwa da tsaki su tabbatar da zaɓe mai gaskiya.
Asali: Legit.ng

