Za a yi Amfani da Yarabawa a Kano a Tarawa Tinubu Kuri'a Miliyan 1
- Ɗan Majalisar Wakilai, Leke Abejide, ya ƙaddamar da shirin wayar da kan al’umma da tallafa wa Yarbawa miliyan 1 da ke Kano domin goyon bayan Bola Tinubu
- Abejide, wanda ke wakiltar mazaɓar Yagba ta Tarayya a jihar Kogi, ya kafa kwamiti mai mutum 27 da zai jagoranci shirin a ƙananan hukumomin Kano 44
- Shirin zai mayar da hankali kan zawarawa, matasa, mata, masu kananan sana’o'i, ’yan kasuwa da sauran mutanen da ke buƙatar tallafin tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Yagba a jihar Kogi, Leke Abejide, ya ƙaddamar da shirin tallafa wa Yarbawa miliyan 1 da ke faɗin jihar Kano tare da neman goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Abejide ya bayyana hakan ne a fadar Sarkin Yarbawa na Kano, bayan ƙaddamar da kwamiti mai mutum 27 da zai tsara tare da gudanar da shirin a ƙananan hukumomin jihar 44.

Source: Facebook
Za a tallafawa Yarabawa
Daily Trust ta wallafa cewa dan majalisar ya ce shirin zai mayar da hankali kan zawarawa, matasa, mata, ’yan kasuwa, marasa galihu da sauran mutanen da ke buƙatar tallafin tattalin arziki.
Ya bukaci mambobin kwamitin da su tabbatar da gaskiya da adalci wajen aiwatar da shirin, domin tallafin ya isa ga mutanen da suke buƙatarsa da gaske.
Abejide ya ce:
“Dole wannan kwamiti ya kasance mai gaskiya da tsayawa kan abin da ya dace. Dole mu tabbatar da cewa tallafin ya isa ga mutanen da suke buƙatarsa da gaske, musamman zawarawa, marasa galihu da sauran masu rauni.”
Alaƙar dan majalisar da Kano
Abejide ya ce alaƙarsa da Kano ta daɗe kafin fara harkokin siyasa, inda ya bayyana cewa ya taɓa zama a jihar tare da gudanar da kasuwanci da kuma kulla alaƙa da mazaunanta.
Ya ce Kano ta kasance muhimmin ɓangare na rayuwarsa, saboda ya zauna a jihar kuma ya gudanar da harkokin kasuwanci a cikinta.

Kara karanta wannan
ACF: An fara wayar da kan 'yan Arewa a Kano kan sayen hannun jari a matatar Dangote
Ya bayyana shirin a matsayin wata dama ta mayar da gudunmawa ga al’umma tare da wayar da kan jama’a domin neman goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Kwamitin zai jagoranci shirin
The Nation ta wallafa cewa mai kula da kwamitin, Seyi Olorunsola, ya yi alkawarin cewa mambobin za su fifita muradun al’umma sama da buƙatun kansu.
Olorunsola ya ce shirin zai samar da hanyar tattaunawa da Yarbawa mazauna Kano tare da tallafa wa dubban mutane da iyalai, musamman zawarawa da masu rauni.
Ya ce kwamitin zai yi aiki tare da masu ruwa da tsaki a al’umma wajen gano waɗanda suka cancanci tallafin da kuma tsara ayyukan shirin a faɗin jihar.
Maganar lafiyar Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da damuwar da wasu ke nunawa kan lafiyarsa bayan ya dawo Najeriya daga hutun aiki da ya yi a ƙasashen Turai.
Tinubu ya ce babu abin da ke damunsa, yana mai bayyana kansa a matsayin mai lafiya da kuma shirye ya ci gaba da gudanar da ayyukansa.
Shugaban ya dawo Najeriya ne daga Faransa bayan ya shafe kusan mako huɗu a Turai, inda ya fara hutun aikinsa a Landan kafin ya koma Paris.
Asali: Legit.ng
