2027: Tsohon Sakataren Gwamnatin Najeriya Ya Sauya Sheka, Ya Bi Tafiyar Su Kwankwaso a NDC

2027: Tsohon Sakataren Gwamnatin Najeriya Ya Sauya Sheka, Ya Bi Tafiyar Su Kwankwaso a NDC

  • Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya koma jam’iyyar NDC watanni uku bayan ya yi murabus daga ADC
  • Lawal ya bayyana goyon bayansa ga tikitin Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso gabanin babban zaɓen 2027
  • Ya ce duk ’yan Najeriya da ke nuna damuwa kan halin da ake ciki na rashin tsaro, yunwa da sauran matsalolin ƙasa su goyi bayan NDC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya koma jam’iyyar NDC watanni uku bayan ya fice daga ADC bisa zargin an yi magudi a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa.

Lawal ya sanar da komawarsa jam’iyyar NDC a Abuja ranar Talata, inda ya bayyana goyon bayansa ga tikitin shugaban ƙasa na Peter Obi da mataimakinsa Rabiu Kwankwaso gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Kungiyar kare hakkin Musulmi a Najeriya ta yi magana kan kama Atiku gabanin zaben 2027

Jam'iyyar NDC.
Jagoran NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson tare da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal Hoto: Seriake Dickson
Source: Facebook

Punch ta ce da yake magana bayan karɓarsa, tsohon SGF ya ce ’yan Najeriya da suka dami da rashin tsaro, yunwa da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta ya kamata su goyi bayan NDC.

“Duk wani ɗan Najeriya da ke da kishin ƙasar nan kuma yake tausayawa wahalhalun da ake fama da su na rashin tsaro, yunwa, jahilci da cututtuka, ba shi da wani zaɓi face shiga jam’iyyar da take da Peter da Kwankwaso a matsayin ’yan takararta.

“Duk wani ɗan Najeriya mai hankali da kishin ƙasa ya kamata ya fahimci hakan. Yanzu ya zama wajibi mu haɗa kai da NDC domin tabbatar da kyakkyawan burin kafa Obi a matsayin shugaban ƙasa da Kwankwaso a matsayin mataimakinsa.

"Don haka, da yardar Allah, muna fatan ranar 29 ga Mayu, 2027, ta zama ranar murnar cimma wannan nasara yadda ya kamata saboda amfanin ƙasa da makomar al’ummomin da za su zo nan gaba.”

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya

NDC Ta Yi Maraba Da Lawal

Yayin da yake karɓar Lawal cikin jam’iyyar, jagoran NDC, Sanata Seriake Dickson, ya bayyana shi a matsayin ƙwararren mai haɗa kan ‘yan siyasa da ɗan fafutuka mai ɗimbin gogewa a siyasar Najeriya.

Ya ce:

“Ba sai an gabatar da Babachir Lawal ba. Shi ne tsohon Sakataren Gwamnatin ƙasarmu, kuma ya yi abin kirki.

"Amma bayan mukaman gwamnati da aka san shi da su, abin da ba a sani ba shi ne cewa ƙwararren mai haɗa kan jama’a ne. Haka kuma, shi ɗan fafutukar siyasa ne.

“Muna farin cikin samun ka domin ka taka rawar jagoranci da kai kaɗai za ka iya takawa a waɗannan matakai. Za ka kula da ayyukan NDC da kamfen ɗinmu a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262