Abin da Atiku Ya Ce Duk da Shan Kayen Dan Takarar Gwamnan ADC a Zaben Osun
- Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi martani da Gwamna Ademola Adeleke ya sake lashe zaɓen gwamnan Osun
- INEC ta bayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen, inda ya samu ƙuri’u 511,067, tare da nasara a ƙananan hukumomi 19.
- Atiku ya ce nasarar Adeleke ta nuna zaɓin al’ummar Osun, yana yaba musu saboda yadda suka shiga zaɓen cikin kwanciyar hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya bayyana gamsuwa da zaben gwamnan Osun.
Atiku ya taya Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, murnar sake lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a jiya Asabar 15 ga watan Agustan 2026.

Source: Facebook
An bayyana hakan ne cikin wani saƙo da Atiku ya wallafa a shafinsa na X a safiyar Lahadi 16 ga watan Agustan 2026.
An sanar da Adeleke wanda ya lashe zaɓe
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Adeleke, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Accord, a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Adeleke ya samu nasara a ƙananan hukumomi 19 daga cikin 30 na Osun, inda ya samu jimillar ƙuri’u 511,067.
Jami’in da ya jagoranci tattara sakamakon zaɓen, kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Oye-Ekiti, Farfesa Joshua Ogunwole, ne ya sanar da sakamakon.
Farfesa Ogunwole ya bayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen da misalin ƙarfe 7:24 na safe ranar Lahadi.

Source: Original
Abin da Atiku ya ce kan zaben Osun
Da yake martani, Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya taya Adeleke murnar sake samun wa’adin mulki.
Atiku ya ce nasarar Adeleke ta nuna zaɓin al’ummar Osun kamar yadda suka bayyana ta hanyar jefa ƙuri’unsu a rumfunan zaɓe.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Gwamna ya gano shirin da APC ta yi wajen tattara sakamakon zaben Osun
Ya yaba wa hukumar INEC kan tabbatar da zabe sahihi wanda zai iya zama zakaran gwajin dafi a babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Ya ce:
“Ina taya Gwamna Ademola Adeleke murnar sake lashe zaɓen Gwamnan Osun.
“Nasararsa ta nuna zaɓin al’ummar Osun kamar yadda suka bayyana a akwatin zaɓe. Ina yaba wa al’ummar jihar saboda himmarsu da kuma shiga zaɓen cikin kwanciyar hankali.
“Ina yi wa Gwamna Adeleke fatan samun ci gaba da nasara yayin da yake ci gaba da yi wa al’ummar jihar hidima.”
Tinubu ya taya Adeleke murnar lashe zabe
Mun ba ku labarin cewa jigo a jam’iyyar Accord, Pelumi Olajengbesi, ya yi magana game da abin kirki da Shugaba Bola Tinubu ya yi masu kafin sanar da sakamako.
Olajengbesi ya yaba wa Tinubu saboda rashin tsoma baki cikin zaben, amma ya ce ba za a bayyana zaben a matsayin cikakken ‘yanci ba.
Ya ce an kama wasu magoya bayan adawa yayin zaben, yayin da Adeleke ya samu kuri’u 511,067, ya doke Bola Oyebamiji na APC mai mulki a Najeriya.
Asali: Legit.ng
