Hankalin Tinubu Ya Koma kan Matatun Mai bayan Karɓar Tawagar NUPENG

Hankalin Tinubu Ya Koma kan Matatun Mai bayan Karɓar Tawagar NUPENG

  • Shugaba Bola Tinubu ya kwakkwaran matakin da gwamantinsa ke shirin dauka wajen farfado da matatun man fetur da suka dade su na lashe kudin kasar
  • Ya ce gwamnatin tarayya za ta gudanar da bincike da tantance matsalolin fasaha, kudi da shugabanci da ke hana matatun aiki yadda ya kamata
  • Shugaban ya kuma yi alkawarin kara bai wa NUPENG dama a shirin CNG,da kuma karban rahoto na musamman da aka kai masa game da lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta bari matatun man fetur na kasar su ci gaba da lalacewa ba, duba da dimbin kudaden da aka zuba wajen kafa da gyara su tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Tinubu zai wallafa yadda aka kashe kudin da aka samu daga cire tallafin man fetur

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja,13 ga watan Agusta, 2026 lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (NUPENG).

Tinubu zai mayar da hankali kan matatun Najeriya
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto:@Dolusegun16
Source: Twitter

Hadimin shugaban a kan sadarwa, Bayo Onanuga ya bayyana a shafin X cewa tawagar a kai masa ziyara karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Salimon Akanni Oladiti, a Fadar Shugaban Kasa.

Bola Tinubu zai waiwayi matatun Najeriya

Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta yi amfani da bincike mai zurfi, sake fasalin tsarin aiki da inganta shugabanci domin dawo da matatun man fetur cikin aiki.

Haka kuma za a yi kokari wajen tabbatar da cewa suna samar da riba da kuma darajar da aka kafa su domin samarwa kasa mai da saukaka al'amura.

Shugaban ya ce matsalolin da ke addabar matatun ba za a magance su da matakan gaggawa na wucin gadi ba, sai dai ta hanyar tsari mai inganci wanda ya dogara da hujjoji da bincike.

Gwamnatin Tinubu za ta nemo kwararru

Shugaban ya ce gwamnati za ta gudanar da cikakken bincike da tantancewar kwararru domin gano matsalolin tsarin gine-gine, ayyukan yau da kullum, kudi da shugabanci da ke kawo cikas ga ayyukan matatun.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Rahoton Amurka ya tabbatar da zargin Atiku kan gwamnatin Tinubu

Tinubu ya ce za a bullo da tsare-tsare game da matatun Najeriya
Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu a taron UN Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Tinubu ya ce:

“Matatun da kuka ambata za su dawo aiki; muna gina ingantaccen tsari, muna sake farfado da su tare da sake tsara tsarin tattalin arzikinsu."

Ya ce ba ya son dora laifin matsalolin kasar kan abubuwan da suka faru a gwamnatocin baya, yana mai cewa nauyin gyara matsalolin ya rataya a kansa a matsayinsa na shugaban kasa.

Tinubu zai yi bayanin cire tallafin fetur

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta bayyana yadda ta yi amfani da kudaden da aka samu bayan cire tallafin man fetur a shekarar farko bayan ya hau mulki.

Bola Tinubu ya ce cire tallafin ya bai wa gwamnati damar karkatar da kudade zuwa wasu bangarorin tattalin arziki da ayyukan more rayuwa da ake gani kuma al'ummar Najeriya su na amfana.

Shugaban ya kuma bukaci NUPENG ta tabbatar da cewa lagwadar amfani da CNG ta isa ga fasinjoji, ba masu motocin dakon kaya kadai ba yadda za a ji sauki a bangaren sufuri da gaske.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng