Kaico: Matashi Ya Aikata Mummunan Abu ga Mahaifinsa Mai Shekara 80 a Katsina

Kaico: Matashi Ya Aikata Mummunan Abu ga Mahaifinsa Mai Shekara 80 a Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Rundunar 'y​an sandan jihar Katsina sun kama Sada Tambai mai shekaru 27 kan zargin kashe mahaifinsa Adamu Tambai, mai shekaru 80, a ƙauyen Mundadu
  • Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Satumba 2026, bayan an samu rahoton cewa tsohon shugaban unguwar Mundadu ya kwanta ba ya motsi a gaban gidansa
  • ‘Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya amsa cewa ya buga mahaifinsa a kai da sanda, yayin da ake ci gaba da bincike.

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar cafke​ wani matashi mai shekaru 27, mai suna Sada Tambai, kan zargin kashe mahaifinsa mai shekaru 80, Adamu Tambai, a ƙauyen Mundadu da ke ƙaramar hukumar Bindawa.

Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Satumba 2026, bayan hedikwatar ‘yan sanda ta Bindawa ta samu kiran gaggawa daga Hakimin Bindawa, Dan Yusufan Katsina.

Kara karanta wannan

Abin kunya: An kama matar aure kan yanayin yadda saurayinta ya mutu a ɗakin Otal

Matashi ya kashe mahaifinsa a Katsina
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An tsinci dattijon kwance a gaban gidansa

A cewar rundunar, hakimin ya sanar da ‘yan sanda cewa an tsinci Adamu Tambai, wanda ya taɓa zama dagacin Mundadu, kwance ba ya motsi a gaban gidansa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Bayan samun rahoton, rundunar ta tura jami’an bincike zuwa wurin domin gudanar da bincike kan lamarin.

Jami’an sun dauki dattijon zuwa asibiti mafi kusa domin samun kulawar likita, amma likita ya tabbatar da rasuwarsa jim kaɗan bayan isarsa.

An kama ɗan mamacin

Rundunar 'yan sandan ta ce binciken farko da jami’anta suka gudanar ya kai ga kama ɗan mamacin, Sada Tambai, domin yi masa tambayoyi kan lamarin.

A cewar ‘yan sandan, wanda ake zargin ya amsa yayin tambayoyi cewa ya bugi mahaifinsa a kai da sanda.

Sai dai rundunar 'yan sandan ta ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Kaico: An kashe budurwa a gidan saurayinta kan rikicin daukar cutar ƙanjamau, HIV

Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin mayar da wanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID).

Kwamishinan ya ce ya kamata a gudanar da bincike cikin tsanaki da zurfi domin gano gaskiyar lamarin.

A wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, rundunar ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Rundunar 'yan sandan ta jihar Katsina ta kuma tabbatar wa jama’a cewa za a tabbatar da an yi adalci bisa sakamakon binciken da aka gudanar.

Matashi ya hallaka mahaifinsa a Katsina
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

'Yan sanda sun cafke matar aure a Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ’yan sandan Abuja ta kama wata matar aure, Rukayat Muhammed, kan zargin hannu a mutuwar wani mutum da ake zargin masoyinta ne a wani otal da ke Gwarimpa, Abuja.

Iyalan mamacin, wanda ba a bayyana sunansa ba, sun fara kai rahoton bacewarsa kafin daga bisani aka gano gawarsa a gefen titin Kubwa kusa da gadar da ke Katampe a ranar 26 ga Agusta, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng