2027: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Hakura da Shiga Zabe, Ya Bi bayan Tinubu
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na tsagin jam'iyyar Accord, Farfesa Christopher Imumolen, ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027
- Imumolen ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da shugabannin jam'iyyar domin marawa shugaban ƙasa Bola Tinubu baya
- Ya ce shugaba Tinubu ya cancanci sake samun goyon baya saboda manufofinsa na sauya tattalin arziki, ƙarfafa matasa da ci gaban ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasar tsagin jam'iyyar Accord, Farfesa Christopher Imumolen, ya janye daga takararsa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Imumolen, wanda shi ne shugaban wani ɓangaren jam'iyyar Accord na ƙasa, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa ya ce ya ɗauki matakin ne bayan ya tattauna da shugabannin jam'iyyar, inda suka yanke shawarar marawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya domin neman wa'adi na biyu.
Dalilin da ya janye daga takara
Imumolen ya bayyana cewa janyewar ba ta samo asali daga wata buƙata ta kansa ba, sai dai saboda kishin ƙasa da kuma fifita haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban Najeriya fiye da burin siyasa.
Ya ce:
"Bayan da na zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Accord a zaɓen fitar da gwani da aka gudanar bisa ƙa'ida, ni tare da shugabannin jam'iyyar muka yanke shawarar janye daga takara tare da cikakken goyon bayan sake zaɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu a 2027."

Source: Facebook
Dalilan goyon bayan Tinubu
Imumolen ya bayyana dalilai 10 da suka sa ya goyi bayan Tinubu, yana mai cewa manufofin shugaban ƙasar sun yi daidai da nasa, musamman a fannonin bunƙasa tattalin arziki, ilimi, ƙarfafa matasa, kasuwanci, masana'antu da ci gaban ƙasa.
Leadership ta wallafa cewa ya ƙara da cewa Tinubu ya nuna jajircewa da ƙwarewa wajen tafiyar da al'amuran siyasa da tattalin arzikin Najeriya duk da ƙalubalen da ake fuskanta.
A cewarsa, shugaban ƙasar ya kuma nuna hikima wajen zaɓen ƙwararrun mutane, haɗa kan jama'a da kuma ɗaukar matakai masu wahala domin amfanin ƙasa.
Imumolen ya bayyana cewa yana da yakinin Tinubu na da damar tabbatar da sauyi mai ɗorewa tare da sake farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya ta hanyar manufofinsa da tsauraran matakan kula da kuɗin gwamnati.
Shehin Darika ya gana da Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Khalifa Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya kai ziyarar ban girma ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa.
Yayin ziyarar, ya miƙa wa shugaban ƙasar gayyatar halartar babban Maulidin Sheikh Ahmad Tijjani, wanda za a gudanar a ranar Lahadi, 9 ga Agustan 2026, a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya yabawa Tinubu bisa kyakkyawar tarba da kuma ƙoƙarin gwamnatinsa wajen inganta zaman lafiya, haɗin kan addinai da kuma haɗin kan Najeriya.
Asali: Legit.ng

