An Samu Sauyi a Dawowar Tinubu, Majiyoyi Sun Sanar da Sabon Lokacin Dawowarsa
- Shugaba Bola Tinubu ya sake dage dawowarsa Najeriya bayan sauya jadawalin tafiyarsa, bayan an sa ran zai dawo a ƙarshen mako
- Tinubu ya shafe makonni yana Turai domin hutun aiki, inda ya kai ziyara London da Paris tare da ganawa da shugabannin ƙasashen waje
- Tsawaita zaman shugaban ƙasar a waje ya haifar da muhawara kan kundin tsarin mulki da kuma ko ya kamata a miƙa ikon shugabanci ga mataimakinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya sake dage dawowarsa ƙasar bayan sauya jadawalin tafiyarsa a minti na ƙarshe.
Tun da farko, ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya a ƙarshen wannan mako, amma zuwa safiyar Lahadi ba a bayyana dalilin sauyin shirin ba.

Source: Facebook
Majiyoyi ne suka sanar da batun dage dawowar shugaban kasar zuwa Najeriya ga jaridar TheCable.
Tinubu zai dawo ranar Talata
Majiyoyin fadar shugaban ƙasa sun shaida cewa Tinubu zai dawo Najeriya bayan shafe makonni yana Turai domin hutun aiki na shekara-shekara.
Ana sa ran shugaban zai fara isa Legas, inda zai shafe kusan mako guda kafin ya zarce Abuja, babban birnin ƙasar.
Sai dai an sake sauya jadawalin, inda ake sa ran yanzu Tinubu zai dawo Najeriya a ranar Talata, 29 ga watan Satumban 2026.
Tinubu ya shafe lokaci a London da Paris
Shugaba Tinubu ya bar Najeriya ranar 30 ga Agusta zuwa London, inda ya fara hutun aiki na makonni uku da fadar shugaban ƙasa ta bayyana a matsayin wani ɓangare na hutun shekara-shekara.
Bayan shafe kusan mako guda a Birtaniya, Tinubu ya zarce zuwa birnin Paris na Faransa.
A lokacin da yake Paris, shugaban ya gana da Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ɗan kasuwa Vincent Bolloré.
A ranar 21 ga Satumba, fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa Tinubu ya tsawaita zamansa a ƙasashen waje da wasu kwanaki, tare da cewa zai dawo Najeriya a ƙarshen mako.
Fadar shugaban ƙasar ta ce Tinubu ya ci gaba da kasancewa cikin hulɗa da jami’an gwamnati a gida, tare da jagorantar harkokin gwamnati duk da kasancewarsa a ƙasashen waje.
Shettima ya wakilci Tinubu
A lokacin da shugaban yake waje, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilci Tinubu a wasu muhimman tarukan gwamnati.
Sai dai Shettima ya tafi New York ranar 20 ga Satumba domin wakiltar Najeriya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.
An fara muhawara kan tsawon zaman Tinubu a waje
Sabon sauyin ranar dawowar Tinubu ya zo ne yayin da ake ci gaba da tambayoyi kan tsawon lokacin da shugaban ya shafe ba ya Najeriya.
Tsawaita zaman nasa a ƙasashen waje ya haifar da muhawara kan kundin tsarin mulki, inda wasu ‘yan adawa ke tambayar ko ya kamata a miƙa ikon shugaban ƙasa ga Shettima bayan shafe kwanaki 21 ba ya cikin ƙasar.
Sashe na 145 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya tanadi cewa shugaban ƙasa zai aika da rubutacciyar sanarwa ga shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai lokacin da zai tafi hutu.

Kara karanta wannan
Za su sha mamaki"; Malamin addini ya hango abin da zai iya fariwa da Tinubu a 2027
Bayan hakan ne mataimakin shugaban ƙasa ke gudanar da ayyukan shugaban ƙasa a matsayin shugaban riƙo.

Source: Twitter
Gbajabiamila bai ci amanar Tinubu ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya ce bai taɓa cin amanar Shugaba Bola Tinubu ba.
Gbajabiamila ya ce zai ci gaba da gudanar da nauyin da ke kansa a Fadar Shugaban Ƙasa duk da abin da ya bayyana a matsayin hare-haren da ake kai masa.
Asali: Legit.ng

