Manyan 'Yan Siyasa 7 Sun Hada kai domin Kifar da Tinubu a 2027

Manyan 'Yan Siyasa 7 Sun Hada kai domin Kifar da Tinubu a 2027

  • Buba Galadima, ya ce tsohon Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, na jagorantar wasu ‘yan adawa 7 da ke kokarin kayar da Shugaba Bola Tinubu
  • Galadima ya bayyana cewa kungiyar ta fara samun ci gaba wajen shirya yadda za ta fuskanci Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027
  • Jigon NDC ya kuma ce yana da yakinin Peter Obi zai samu nasara idan aka gudanar da zaben cikin ’yanci, gaskiya da adalci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Jigon jam’iyyar Nigeria NDC, Buba Galadima, ya yi ikirarin cewa tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, na aiki tare da wasu ‘yan adawa domin kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Buba Galadima na cikin 'yan siyasar da suka sauya sheka zuwa NDC tare da jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta dauki mataki ganin Tinubu ya kara hutu ba tare da ba Kashim mulki ba

Buba Galadima
Jagoran NDC, Buba Galadima. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Source: Twitter

Buba Galadima ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television a shirin Politics Today, inda ya ce mutane 7 ne ke cikin kungiyar da Fayemi ke jagoranta.

Mutane 7 na adawa da Tinubu

Galadima ya ce shi ma yana cikin kungiyar ‘yan siyasar adawa 7 da ke kokarin hada kai domin tinkarar Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.

Ya ce kungiyar na samun ci gaba a kokarinta, yana mai cewa manufarsu ita ce kayar da Shugaba Tinubu a zaben.

“Ni ma ina so in bayyana a bainar jama’a cewa ina cikin kungiyar ‘yan adawa 7 da ke karkashin jagorancin Gwamna Kayode Fayemi, kuma muna samun ci gaba,”

In ji Buba Galadima.

Da aka tambaye shi abin da suke aiki a kai, sai ya amsa kai tsaye cewa suna aiki ne domin “kayar da Tinubu”.

Hadimin Wike ya nemi bayani

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya fadi wanda zai iya nasara a 2027, ya cire Tinubu a lissafi

Daily Post ta wallafa cewa bayan bayyana kalaman Galadima, wani hadimi na musamman ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya wallafa faifan hirar a shafinsa.

Ya ce ba zai yarda da ikirarin Galadima ba har sai Fayemi ya fito ya karyata cewa yana cikin kungiyar da ake zargin tana aiki domin kayar da Tinubu.

Kayode Fayemi
Kayode Fayemi na magana a wajen taro. Hoto: Kayode Fayemi
Source: Facebook

Fayemi na daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC, amma ya sha sukar wasu manufofi da matakan jam’iyyar mai mulki a lokuta daban-daban.

APC ta taba gargadin Fayemi

A ranar 23 ga Maris 2026, Sakataren Jam’iyyar APC na Kasa ya bukaci Fayemi ya yi murabus daga jam’iyyar idan har ya daina amincewa da akidunta.

Jam’iyyar ta kuma gargadi tsohon gwamnan cewa za ta iya daukar matakin ladabtarwa a kansa bisa zargin ayyukan da suka saba da muradun jam’iyyar.

Sai dai ikirarin Galadima na cewa Fayemi na jagorantar kungiyar ‘yan adawa 7 ya fito ne daga kalamansa yayin hirar, yayin da Fayemi bai bayyana matsayarsa kan wannan ikirari a bayanan da aka ambata ba.

Magana kan zaben 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa Buba Galadima ya ce Allah da Shugaba Bola Tinubu ne kadai suka san abin da zai faru a zaben shugaban kasa na 2027.

Kara karanta wannan

Da gaske ne mataimakin gwamna ya ce a yi wa Tinubu ruwan duwatsu?

Ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai, inda ya tattauna kan shirin jam’iyyar NDC da tikitin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.

Da aka tambaye shi ko yana sa ran za a gudanar da zaben cikin ’yanci da adalci, Galadima ya nuna shakku, yana mai cewa wasu abubuwan da ke faruwa a siyasar kasar sun sanya ‘yan adawa cikin damuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng