Pantami Ya Shirya wa 2027 da Kyau, Ya Soma Jefa wa APC Maganganu a Dunkule

Pantami Ya Shirya wa 2027 da Kyau, Ya Soma Jefa wa APC Maganganu a Dunkule

  • Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya zargi masu rike da madafun iko a yau da handame dukiyar al’ummar da aka ba su amana
  • Malamin Musuluncin da yake neman zama gwamnan jihar Gombe ya gargadi masu mulki cewa murde zabe ba zai yiwu ba
  • ‘Dan takaran PDP a zaben 2027 ya ba ‘yan APC shawara su nemi yafiyar mutane saboda sun saba alkawuran da suka dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Gombe - Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi maganganu da-dama da ya ziyarci karamar hukumar Balanga a jihar Gombe kwanan nan.

Da jin wadannan maganganu, wasu suka shiga tofa albarkacin bakinsu, suna cewa lallai malamin ya rikida zuwa cikakken ‘dan siyasa.

Isa Pantami
Isa Ali Ibrahim Pantami yana jawabi da hoton 'dan takaran wajen taron PDP a Gombe: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Isa Ali Pantami ya caccaki masu mulkin Gombe

A Facebook, Abba Sani Pantami ya daura bidiyon jawabin ‘dan takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam’iyyar PDP mai adawa.

Kara karanta wannan

Abin da shugabannin jami’ar MAUN suka fada game da Nasa’i Gwadabe ya fito

Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi zargin cewa wasu sun samu mukami sun ci amanar al’umma kuma sun kwashe dukiya su kadai.

Bai kama suna ba, amma ‘dan adawar ya yi zargin cewa an fada wa dattawan Gombe bakaken maganganu kuma ana yi masu barazana.

Pantami yana ganin lokacin magudi ya wuce

Ganin yadda ya jero kalaman, yana cewa wanda ake zargi da shi da ‘dan takararsa ba su isa su yi magudi ba, da alama da gwamna Gombe yake.

Ya bayyana cewa ba a isa a murde zabe, a fitar da sakamako na bogi ba, ya ce masu wannan tunani sun cancanci a kai su gidan mahaukata.

"Idan ka ji wasu mutane da ba su san shirin da muka yi ba, wai mutum sai ya zauna - ya san ya ci amanar al’umma, ya yi alkawari ya karya, ya ba wa kan sa sarauta ta ‘ci kai kadai’…
"Kuma a haka an zagi iyayen kasa da dattawa, an yi masu muzurai, gidajen da suke ciki ana barazana ga gidajen, ana cewa sai sun biya kudi, kuma a haka mutum wai ya yi tunani mutum da shi da ‘dan takararsa, za su shiga daki su rubuta abin da suke so su fito."

Kara karanta wannan

2027: Alkawarin da Pantami ya yi wa kiristoci a Gombe da ya kai ziyara coci

- Isa Ali Pantami

Shirin da Pantami yake yi wa zaben Gombe

A bidiyon, Isa Pantami ya ce masu ganin akwai yiwuwar a murde zaben 2027, sun jahilci wayewar al’ummar yau kuma ba su san dokar kasa ba.

Malamin ya ce:

“Babu mutum daya da ya isa ya rubuta abin da ba shi aka zaba ba. Babu wanda ya isa ya jirkita abin da aka zaba.
“Wanda zai iya yin wannan shi ne mala’ika, kuma mala’ika ba zai yi ba. Amma a ‘dan adam babu wanda ya isa ya yi da iznin Allah. Ba a haifi mutumin ba.”

Pantami ya nuna cewa sun yi tsari kuma sun san fasahar yau sannan za su cigaba da wayar da kan al’umma idan lokacin yakin neman zabe ya yi.

'Dan takaran PDP ya jefa wa gwamnatin APC maganganu

Shehin ya ba wadanda ke mulki shawarar su fita su ba talakawa hakuri, su fada masu sun ci amanarsu kuma suna neman Gombawa su yafe masu.

Kara karanta wannan

2027: Pantami ya yi zargin an shirya kai wa tawagarsa hari a Gombe

Ya yi zargin an karya alkawuran da aka dauka, sannan aka talauta ‘yan kwangila, yana tuhumar masu mulki da zama ‘yan kwangila a jihar Gombe.

A cewar Pantami, mutum guda ne yake tsara kasafin kudi, ya gabatar, kuma ya amince da shi, sannan ya bada kwangila sanna shi zai yi kwangilar.

Hatta wuraren da za a saye kayan aiki da inda za a yi kwangilar, Pantami ya fada wa mutanen garin Balanga cewa mutum daya ne yake yi a gwamnati.

Pantami
Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami a gajiye wajen wani taro a jihar Gombe: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Meyasa Sheikh Pantami ya shiga siyasa?

‘Dan takaran ya zargi masu mulki da rashin aiwatar da tsarin da suka dauko, kuma a nan ya fadi babban abin da ya shigar da shi cikin siyasa.

Wani zargi da ya yi shi ne an jefa mutane cikin talauci, Pantami ya ce in ban da saboda abubuwa sun cabe, da ba za su shiga siyasa ba.

Farfesan ya ce ba za su zura idanu ana barna ba don haka suke son kawo gyara ta fuskar tattalin arziki, samar da ayyukan yi da tsaro.

“Har ga Allah matsalar matasa, iyaye mata, tsaro, tattalin arziki su ne da suka tilasta muka shiga cikin wannan tsari.”

Kara karanta wannan

Mijin dalibar Ma'un ya zayyano abin da ya faru tsakaninsu da malamin jami’a a Kano

Idan Pantami ya samu yadda yake so, ya sha alwashin taimaka wa iyaye mata da ke gidaje.

Pantami bai da mu’amala,’ - Baban Chinedu

An ji labari cewa Malam Yusuf Haruna wato Baban Chinedu ya ce tsohon ministan sadarwa, Isa Pantami zai iya rike Najeriya, sai dai akwai gyara a lamarin shi.

Baban Chinedu ya fadi inda Pantami ya samu matsala a siyasa duk da irin tarin ilminsa da kuma kokarin da ya nuna lokacin da aka ba shi mukamai a baya.

Tsohon 'dan wasan kwaikwayon wanda yanazu ya shiga fagen malanta ya ba 'dan takarar gwamnan shawara ya yi hakuri ya gyara huldarsa da mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng