Siyasar Gombe: Sheikh Pantami Ya Gana da Sanata Yaro a Abuja
- Harkokin siyasar jihar Gombe na cigaba da daukar hankali musamman bayan komawar Sheikh Isa Ali Pantami jam'iyyar PDP
- Sanata Anthony Yaro da ke wakiltar Gombe ta Kudu a majalisar dattawa ya ziyarci Sheikh Pantami a ofishin shi da ke birnin tarayya Abuja
- Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana muhimman abubuwan da suka tattauna a zaman da suka yi da Sanata Anthony Yaro ranar Talata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Sanata Anthony Siyako Yaro mai wakiltar mazabar Gombe ta Kudu ya kai ziyarar girmamawa ga Sheikh Isa Ali Pantami a ofishinsa a ranar Talata.
Bayan zaman da suka yi, Pantami ya fadi abubuwan da suka tattauna a game da muhimman batutuwan ci gaban al’ummar jihar Gombe.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano bayanin da Sheikh Isa Ali Pantami ya yi ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 3 ga watan Yuni.
Tattaunawar Isa Pantami da Sanata Yaro
Pantami ya ce taron ya mayar da hankali ne kan fannoni masu muhimmanci da suka haɗa da ilimi, noman zamani da kuma samar da ayyukan yi da bunƙasa matasa da mata.
Jagororin biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan hanyoyin da za su taimaka wajen samar da ci gaba mai ɗorewa tare da faɗaɗa damar koyon sana’o’i da samun hanyoyin bunƙasa tattalin arziki a faɗin jihar Gombe.
Farfesa Pantami ya ba Yaro kyautar littafi
A yayin ziyarar, Sheikh Isa Ali Pantami ya bai wa Sanata Yaro kwafin littafin da ya rubuta kan gudunmawar da ya bayar.
Littafin ya ƙunshi bayanai kan ayyuka sama da 241 da aka aiwatar a ƙananan hukumomi 11 na Jihar Gombe, tare da bayyana wuraren da aka gudanar da kowane aiki.
A ƙarshe, Sheikh Pantami ya bayyana godiyarsa ga Sanata Yaro bisa wannan ziyara da kuma tattaunawar da suka yi.
Ya ce:
“Ƙoƙarinka na tattaunawa kan batutuwan da suka shafi rayuwar al’ummarmu abin yabawa ne. Ina fatan za mu ci gaba da haɗa kai domin amfanin jama’ar Jihar Gombe.”
Bayanin Sanata Anthony Yaro
A nasa bangaren, Sanata Yaro ya gode wa Farfesa Pantami bisa bayanan da ya gabatar masa, tare da jaddada aniyarsa ta ci gaba da aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki domin ciyar da ci gaban Gombe ta Kudu da kuma jihar baki ɗaya gaba.
Haka kuma, su biyun sun yaba wa Ibrahim Hassan Dankwambo bisa tawali’unsa, sadaukarwarsa da kuma jajircewarsa wajen yi wa al’ummar Jihar Gombe hidima.

Source: Facebook
Sun bayyana cewa Sanata Dankwambo ya nuna a aikace cewa shi shugaba ne na musamman wanda ke girmama kowa tare da kula da jin daɗin jama’a.
Dalilin sukar PDP da Pantami ya yi
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi karin bayani kan sukar PDP da ya yi a shekarun baya.
A bayanin da Pantami ya yi, ya ce ya yi wa PDP muguwar addu'a ne a lokacin da tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro ya yi wata magana.
Ya ce Andrew Azazi ya taba cewa jam'iyyar PDP ce ke kara ruruta matsalar tsaron da aka fuskanta a shekarun baya, musamman a 2012.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

