Abin da Shugabannin Jami’ar MAUN Suka Fada game da Nasa’i Gwadabe Ya Fito
- Dr. Nasa’i Muhammad Gwadabe bai da wata alaka a yanzu da jami’ar nan ta Maryam Abacha ta Kano
- Mahukuntan MAUN sun ce kwantiragin malamin ya kare tun a Afrilun 2026 amma sun yi zaman lafiya da shi
- Jami’ar ta ce game da duba aikin Sa’adatu Kabir Uba kuwa, kwantan aiki ne da ya kamata a gama tun tuni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - An tuntubi jami’ar Maryam Abacha da ke Najeriya domin jin matsayin malamin nan, Nasa’i Muhammad Gwadabe a wajen ta.
‘Yan jarida sun nemi karin haske daga mahukuntan wannan jami’a ta kudi ne biyo bayan zargin da aka yi wa malamin da neman matar aure.

Source: Facebook
'Dan jarida ya ziyarci jami'ar Maryam Abacha Kano
Gidan rediyon Lumana International ya samu jin ta bakin shugabannin jami’ar ta Kano game da alakarta da Dr. Nasa’i Muhammad Gwadabe.
Malam Yakubu Musa Fagge ya ziyarci makarantar bayan yi magana da malamin da aka yi wa duka da kuma mijin dalibar da abin ya shafa.
Jami’ar ta shaida wa ‘dan jaridar cewa a halin yanzu Dr. Nasa’i Gwadabe ba ma’aikacinta ba ne, kwantiraginsa ya kare a Afrilun 2026.
Bayanan shugabannin makarantar sun tabbatar da an san da zaman Nasa’i Gwadabe a matsayin wanda ya yi aikin wucin-gadi kuma ya gama.
Yadda MAUN ke yaki da neman dalibai
Da farko dai ta ce MAUN ba ta daukar ma’aikaci ko dalibin mai mugun hali kuma har aka rabu, ba a san Gwadabe da wani aikin assha ba.
Idan da kuwa an same shi da barna, da an yi waje da shi domin jami’ar ta yi ikirarin ba ta sakaci wajen samar da yanayin karatu da ya dace.

Source: Facebook
MAUN ta kafa hujja da yadda wanda ya assasata, Farfesa Adamu A. Gwarzo ya dauki zafi a kan malaman da aka samu suna neman dalibansu
Wani fai-fan bidiyo ya nuna Farfesa Gwarzo yana alkawarin N5m ga duk wata ta kawo karar malamin jami’ar da yake neman ta da soyayya.
Wasiku sun tabbatar da aikin malamin ya kare
Baya ga haka, jami’ar ta nuna hoton wasikar da Dr. Gwadabe ya aiko yana neman a sabunta kwantiraginsa bayan karewarsa a shekarar nan.
Sai dai wata takarda da ta fito daga Farfesa Muhammad Israr a karshen Afrilu, ta tabbatar da MA’UN ba za ta dauke shi ba, ba tare da fadin dalili ba.
Duk wannan abin da ake yi, jami’ar ta MAUN ba ta ce malamin ya aikata laifi ba, illa iyaka dai ta bayyana cewa alakarsu da shi ta kare a Afrilu.
Ya aka yi Nasai Gwadabe bai yaye dalibarsa ba?
Malamin ya gama aiki da jami’ar tun kafin wannan zargi ya taso. Wannan ya jawo aka nemi jin ya aka yi har yanzu bai gama yaye dalibansa ba.
A nan jami’ar ta ce ya kamata babban malamin ya gama duba binciken da dalibar ajin karshen ta ke yi tun kafin watan Mayun shekarar nan.

Kara karanta wannan
Mijin dalibar Ma'un ya zayyano abin da ya faru tsakaninsu da malamin jami’a a Kano
Tunda ba su da hurumi a kan wanda ake zargi, jami’ar ta bada shawarar jami’an tsaro su yi bincike domin a hukunta duk wanda bai da gaskiya.
A game da batun Hajiya Sa’adatu Kabir Uba kuwa, jami’ar ta kafa kwamiti ya binciki kokenta da nufin bi mata hakki idan an ci mata zarafi.
Malami da ake zargi da lalata ya bude baki
Labarin nan ya ce Nasa'i Muhammad Gwadabe, malamin da ake zargi da neman lalata da dalibarsa mai aure, Sa'adatu Kabir Uba ya karyata zargin.
Dr. Gwadabe ya rantse da Allah cewa babu wata alaka ta lalata ko neman matar aure tsakaninsa da dalibar kamar yadda aka rika yadawa a duniya.
Ya ce an tura masa dalibar ne don ta gudanar da binciken digiri a karkashin kulawarsa a watan Nuwamban 2025, ba shekaru biyu da ake fada ba.
Asali: Legit.ng

