Mijin Dalibar Ma'un Ya Zayyano Abin da Ya Faru tsakaninsu da Malamin Jami’a a Kano
- Usman Ibrahim ya yi bayanin yadda ta kaya tsakanin su da malamin matarsa, Nasa’i Muhammad Gwadabe
- Magidancin ya karyata malamin jami’ar da aka yi wa duka saboda zargin yana neman matar aure da sunan karatu
- Da aka zanta da shi, Usman Ibrahim ya zargi Dr. Gwadabe da bibiyar mai dakin shi duk da tana gidan aure
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Ana cigaba da yin maganganu game da malamin jami’ar da aka lakada wa duka bisa zargin yana neman matar aure a garin Kano.
‘Yan jarida sun yi magana da mijin dalibar wannan malami domin jin ta bakinsu ganin Nasa’i Muhammad Gwadabe ya wanke kan shi.

Source: Facebook
An yi hira da mijin Sa'adatu Kabir Uba
Tashar Lumana ta zanta da Malam Usman Ibrahim wanda shi ne mai gidan dalibar da ake ta magana a kan ta watau Sa’ada Kabiru Uba.
Shi dai Malam Usman Ibrahim ya dauko yadda abin ya faro tiryan-tiryan tun daga wata Alhamis 2 ga watan Yuli 2027 a jami’ar Baba Ahmad.
A ranar ne ya ce mai dakinsa ta fada masa za ta je wajen malamin jami’ar nasu, kuma ya duba aikin tare da yin gyare-gyaren da suka dace.
Nasa'i Gwadabe ya yaba da kyawun matar aure
Bayan ya yi gyara ta yi godiya za ta tafi, Usman ya ce sai Dr. Nasa’i Gwadabe ya nemi matarsa ta tsaya zai rubuta mata wani abu a takarda.
Magidancin ya ce a nan malamin makarantar ya dauko farar takarda yake rubuta mata cewa ko ‘ta san tana da kyau?’, ta amsa masa da ‘Eh’
Daga nan ne ya fara nuna sha’awar su hadu wata rana, lamarin da ya fara fita daga karatu, a haka ne ya kawo shawarar a je shan ‘ice cream’.
Mijin Sa’adatu Uba ya bayyana cewa daga nan ne ya ce zai yi mata magana a whatsApp duk da ta je wajen shi da yaro har da na goye.
Usman Ibrahim ya shaida cewa matar tasa ta yi nasarar daukar hoton takardar da malamin yake rubuta mata cewa ita kyakkyawar mace ce.
Rabuwar ta da malamin ya ke da wuya, sai ta kwashe labarin abin da ya faru ta fada masa kuma ta aiko masa da hoton wannan takarda.
Duk da an yi ba za ta fada wa kowa ba, Sa’adatu ta ankarar da mahaifiyarta, wanda ita kuma ta nemi a canza mata wanda zai duba aikinta.
Da maganar ta taso a kan malamin a gida ne sai shi mijin ya rika amfani da kafar WhatsApp, yana zantawa da Dr. Gwadabe kamar matar ce.
Haduwar Nasa'i Gwadabe da Sa'adatu da mijinta
Bayan nan, a cewar Usman Ibrahim sai malamin makarantar ya nemi lokacin da zai gana da ita, ya bukaci a hadu da maraicen ranar Juma’a.
Duk wannan, mijin wannan baiwar Allah ne ya rika magana da malamin da wayar mai dakinsa, kuma ya karfafa zargin da ake yi masa.
Da aka bukaci a zo da kundin binciken da ake yi sai malamin jami’ar ya ce babu bukatar domin ba ganawar aikin makaranta za a yi ba.
A hirar da aka yi da shi, magidancin ya ce daga nan ne suka shirya hadu wa da malamin a jami’ar Bayero, kuma suka tafi su biyu a mota.

Source: Facebook
Da aka tambaye shi ko matarsa ta sanar da malamin nasu tana da aure, sai Usman Ibrahim ya ce ai ya gan ta da karamin yaro da ake shayarwa.
Bayan Nasa’i Gwadabe ya shiga mota kuma ya lura mai gidan yana kujerar baya, sai ya nemi ya tsare, a dalilin haka ne shi Usman ya shako shi.
Abin da mijin matar ya fada shi ne, ya umarci Sa’adatu Uba ta je waje ta tara masu jama’a, akasin abin da Gwadabe ya fada da aka zanta da shi.
A karshen hirar da ta ke Facebook, ya karyata zargin da ake yi masa na lakada wa malamin jami’ar duka, ya rantse da Allah ba a yi hakan ba.
Shi dai ya ce ya rike shi ne saboda gudun ya tsere, amma babu shi a lakada masa duka, ya ce mutanen da ke kewayen wurin ne suka duke shi.

Kara karanta wannan
'Yan Bindiga: Kungiyar duniya ta yi wuf ta yi magana da jin an cafke malami a Katsina
Duk da shi ma ya yarda babu abin da ya kai ga shiga tsakaninsu, wannan mutumi ya wanke matarsa daga zargin bude wa malamin kofar bibiyarta.
Ko da aka tambaye shi mai yake bukata, ya nuna za su so a yi sulhu domin hakan alheri ne, yanzu dai malamin yana jinya a gadon asibiti.
Nasa'i Gwadabe ya ce bai nemi Sa'adatu ba
Ana da labari cewa Dr. Nasa'i Muhammad Gwadabe ya musanta zargin da ake yi masa na neman yin lalata da ɗalibarsa mai aure, ya ce kage ne aka yi masa.
Malamin ya bayyana cewa jami'ar Maryam Abacha (MAUN) ce ta ba shi alhakin kundin digiri na Sa'adatu Kabir Uba duk da bai koyar da masu digirin farko.
Gwadabe ya ce ɗalibar ce ta matsa lamba cewa tana son su haɗu don ya ƙara yi mata bayanin gyare-gyaren da ya yi mata a aikinta, akasin zargin da ake yi.
Asali: Legit.ng


