Matakin EFCC: Abin da Tinubu Ya Fada Wa Gwamna Adeleke bayan Kiransa a Waya

Matakin EFCC: Abin da Tinubu Ya Fada Wa Gwamna Adeleke bayan Kiransa a Waya

  • Shugaba Bola Tinubu ya kira gwamnan Osun, Ademola Adeleke, inda ya tabbatar masa cewa ya umarci EFCC ta janye umarnin kotu kan daskarar da asusun gwamnatin jihar
  • Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Tinubu ya ba EFCC umarni ta dauki matakan soke umarnin kotun da ya hana amfani da asusun gwamnatin Osun
  • Matakin daskarar da asusun ya jawo ce-ce-ku-ce, inda masu suka ke zargin cewa yana da alaka da zaben gwamnan Osun da za a gudanar ranar 15 ga Agusta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fadar shugaban kasa a Najeriya ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kira Gwamna Ademola Adeleke a waya.

Shugaba Bola Tinubu ya kira gwamna Adeleke, domin tabbatar masa da umarnin da ya bayar ga hukumar EFCC bayan matakin da ta dauka.

Kara karanta wannan

"Na ji kunya": Tinubu ya ba EFCC umarnin bude asusun gwamnatin Osun da aka rufe

Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis.

Tinubu ya fasa masa cewa ya umarci Hukumar EFCC ta dauki matakan janye umarnin kotu da ya daskarar da asusun gwamnatin jihar.

A cewar Onanuga, Shugaba Tinubu ya shaida wa Adeleke cewa ya bayar da umarni ga EFCC ta dauki matakan da suka dace domin soke umarnin kotun da ya hana gwamnatin Osun amfani da asusun nata.

Sanarwar kiran wayar ta fito ne bayan fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Tinubu ya umarci EFCC da ta dauki matakan janye umarnin kotun da ya shafi asusun gwamnatin Osun.

A ranar Laraba, EFCC ta tabbatar da cewa ta sa aka daskarar da asusun gwamnatin Osun saboda zargin cewa ana shirin amfani da shi wajen aikata wasu ayyukan da suka saba wa doka.

Sai dai matakin ya fuskanci suka daga mutane da dama a Najeriya, wadanda suka bayyana cewa hakan na iya zama katsalandan daga gwamnatin tarayya gabanin zaben gwamnan Osun.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya yi barazana ga Tinubu, zai yi murabus daga jam'iyya mai mulki

Masu sukar sun nuna cewa lokacin daukar wannan mataki ya haifar da tambayoyi, musamman ganin cewa za a gudanar da zaben gwamnan Osun ranar 15 ga Agusta.

A halin yanzu, babban abokin hamayyar Gwamna Ademola Adeleke a zaben shi ne Bola Oyebamiji, dan takarar jam'iyyar APC, wadda Shugaba Tinubu ke jagoranta a matakin kasa.

Rahoton ya ce ana sa ran karin bayanai kan wannan lamari yayin da ake ci gaba da bibiyar matakan da EFCC za ta dauka bayan umarnin shugaban kasa.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.