Dalilin da Ya Sa Daliban Wasu Jihohin Najeriya ba Su Ga Sakamakon Jarabawar WAEC ba
- Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta WAEC ta tabbatar da cewa ba a saki sakamakon jarabawar daliban wasu jihohi ba
- WAEC ta bayyana cewa ta rike sakamakon jarabawar 2026 ta wasu jihohi ne saboda bashin da take bin su
- Hukumar ta rike sakamakon dalibai 167,486 saboda zargin magudin jarrabawa, inda ta ce hakan ya nuna an samu raguwar magudi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawonshekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Makarantar Sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC) ta sanar da cewa ta rike sakamakon daliban wasu jihohi a Najeriya.
WAEC ta tabbatar da cewa daliban WASSCE na shekarar 2026 na wasu jihohi ba za su ga sakamakon jarabawarsu ba ko da sun shiga shafin da aka tanada.

Source: Facebook
Shugaban Ofishin WAEC na Kasa a Najeriya, Dakta Amos Josiah Dangut, ne ya bayyana hakan yayin sanar da sakamakon jarrabawar jiya Laraba, cewar rahoton Vanguard.
Dalilin rike sakamakon WAEC a wasu jihohi
Ya ce hukumar ta rike jarabawar wasu jihohi ne saboda tana bin gwamnatocin jihohin ba shi, kuma ba za a saki sakamakon ba har sai suk biya wannan ba shi.
Ya ce:
"Ba sai na sake jaddada ba, ba za mu saki sakamakon daliban da WAEC ke bik gwamnatocin jihohinsu bashi ba har sai an biya bashin."
Ya roki gwamnatocin da abin ya shafa da su gaggauta biyan kudaden domin bai wa daliban damar samun sakamakonsu. Sai dai hukumar ba ta bayyana sunayen jihohin da abin ya shafa ba.
WAEC ta rike sakamakon dalibai 167,486
WAEC ta kuma sanar da cewa ta rike sakamakon dalibai 167,486, wanda ya kai kashi 8.59 cikin 100 na wadanda suka rubuta jarrabawar, saboda zargin magudin jarrabawa.
Hukumar ta ce wannan ya nuna raguwar kashi 1.11 idan aka kwatanta da kashi 9.7 cikin 100 da aka samu a shekarar 2025.
Dakta Dangut ya ce:
"Ci gaba da shiga da wayoyin hannu dakin jarrabawa duk da haramcin da aka yi, da kuma shirya magudi a wasu makarantu, na daga cikin manyan matsalolin da muke fuskanta."
Ya kara da cewa an kama wasu masu kula da jarrabawa da masu sa ido da ake zargi da taimakawa dalibai wajen aikata magudi.

Source: Twitter
Dalibai masu bukata ta musamman
Hukumar ta bayyana cewa dalibai 1,213 masu bukata ta musamman sun rubuta jarrabawar, ciki har da dalibai makafi 137 da kurame 491, cewar rahoton The Cable.
Hukumar ta kuma kaddamar da wani sabon shafi da dalibai za su iya amfani da shi wajen sayen lambobin duba jarabawa na e-PIN kai tsaye..
An gudanar da jarrabawar daga ranar 24 ga Afrilu zuwa 19 ga Yuni, 2026, inda malamai masu gyaran takardu 102,708 suka yi aikin gyara a cibiyoyi 88.
WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2026
Tun farko, kun ji cewa hukumar WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar WASSCE ta 2026, inda sama da ɗalibai miliyan 1.2 suka samu aƙalla darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.
Hukumar ta bukaci ɗalibai su mallaki PIN sannan su duba sakamakonsu ta shafukan intanet na WAEC .
Asali: Legit.ng

