2027: Alkawarin da Pantami Ya Yi wa Kiristoci a Gombe da Ya Kai Ziyara Coci
- Isa Ali Ibrahim Pantami da mutanen shi sun ziyarci wani coci a kusa da gidanshi a ranar Lahadi da ta gabata
- Malamin addinin ya bayyana cewa saukin hakkin makwabtaka ya kai shi cocin ba yakin neman zaben gwamna ba
- Pantami ya yi alkawarin za su bada gudumuwarsu wajen ganin an sake gina wanna majami’a da ta kone
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Gombe - Isa Ali Ibrahim Pantami ya shiga siyasa gadan-gadan kuma yanzu haka malamin yana neman takarar gwamnan jihar Gombe.
A makon da ya gabata, wani bidiyo ya rika yawo a kafofin sada zumunta na zamani, aka ga Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya shiga coci.

Source: Facebook
Sheikh Isa Pantami ya je coci a Gombe
A dandalin Facebook, shafin Prof. Isa Pantami ya daura bidiyon wannan ziyara zuwa cocin ECWA a garin Gombe dauke da jawabin da aka yi.
Jaridar Legit Hausa ta saurari jawabin ‘dan takarar PDP inda ya bayyana cewa ya zo wurinsa ne domin yi masu jajen gobara da ta yi masu barna.
Isa Ali Ibrahim Pantami ya kuma bayyana cewa sun wakilci jagoran PDP na Gombe wato Sanata Ibrahim H. Dankwambo OON wajen wannan jaje.
“Na farko na zo ne in tausaya maku, ba yakin neman zabe mu ka zo ba. Ni makwabcinku ne, gida na bai da nisa da nan.
An sanar da ni game da gobarar, sai dukkanmu ‘yan tawagar nan da shugabannin nan muka amince mu zo nan, mu jajanta maku.
- Sheikh Isa Ali Pantami OON
Hudubar Isa Pantami a cocin ECWA
Farfesa Isa Pantami ya tuna wa masu ibada a cocin cewa su tuna Ubangiji ba ya kuskure, ya ce dole a rungumi kaddarar wannan gobara.
Baya ga haka, ya tuna wa kiristocin da abokan tafiyarsa yadda littafin Bible ya koyar da juriya idan aka ci karo da halin kunci da wahala.
Malamin Musuluncin ya jawo da surah ta James, babi na farko a cikin ayoyi ukun farko.

Kara karanta wannan
Mijin dalibar Ma'un ya zayyano abin da ya faru tsakaninsu da malamin jami’a a Kano
A littafin mai tsarki wajen Kiristoci, Pantami ya fadakar da jama’a sai jarrabawa daga Ubangiji ta zo ne sannan mutum zai samu cikakkiyar kamala.
Farfesan ya ce har a surah ta Peter, Bible ya yi magana game da hakuri da jarrabawa. Daga cikin wannan jarrabawa ita ce konewar cocinsu.
Bayanin Bible ya yi kama da na Kur'ani
Kuma abin da Bible ya fada ya zo daidai da abin da yake cikin Suratul Baqarah a ayoyi na 155, 156 da 157 game da jarabtar bayi a Kur’ani.
Allah SWT ya ce zai jarrabi bayinSa da yunwa, tsoro da asarar dukiya, a karshe sai aka yi bushara ga wadanda suka jure kuma suka yi hakuri.
A karshe ya kira masu ibadan da abokai, makwabta kuma ‘yanuwa tare da alkawarin jagororin tafiyarsa za su bada gudumuwar sake gina cocin.

Source: Getty Images
Su wane ne 'yan rakiyar Isa Pantami?
A tawagarsa akwai Mataimakin shugaban PDP na Gombe, Ibrahim Muhammad Danzumi da sakataren PDP na reshen jihar, Adamu Abubakar.
Manyan sakatarori da lauyoyin jam’iyyar PDP na reshen Gombe da babban likita, Farfesa Muhammad Bello Abubakar suna cikin ‘yan rakiyarsa.

Kara karanta wannan
PFIPC: Shugaban hukumar bogi ya soki binciken ICPC, ya aika sako ga Shugaba Tinubu
Farfesa Pantami ya je cocin da masu sarauta irinsu Cika-soron Gombe da Kangiwan Gombe wanda yake yi wa PDP takarar Sanata a zaben 2023.
Bidiyon ziyarar daga shafin Tahir Muhammad Saleh:
'Dan majalisar tarayya da ya koma shago
Hon. Abubakar Cika Adamu cike yake da da-na-sani saboda kujerar Majalisar tarayya da ya rike na shekaru hudu kamar yadda aka ji labari.
Yanzu haka wannan 'dan siyasa ya koma kasuwa, yana cewa dama shi tun farko mutane ne suka saya masa fam a 2015 ya wakilce su a APC.
Abubakar Cika ya hakura da kujerar Majalisar tarayya, ya zabi ya koma kasuwa saboda a cewarsa bai ga amfanin wakilcin da ya yi a Abuja ba.
Asali: Legit.ng
