Yadda Kiristoci Suka Fi Musulmi Cin Moryar Mulkin Tinubu a Najeriya

Yadda Kiristoci Suka Fi Musulmi Cin Moryar Mulkin Tinubu a Najeriya

  • Kungiyar matasan Musulmi ta NACOMYO ta yi magana game da korafin da ake kan tikitin Musulmi da Musulmi a Najeriya
  • Kungiyar ta kare tsarin takarar Musulmi da Musulmi na Bola Tinubu, tana mai cewa adawar wasu Kirista kafin zaben 2027 munafunci ne
  • NACOMYO ta bukaci kungiyoyin addini su ci gaba da bai wa gwamnati shawara da addu’a domin ci gaban Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar matasan Musulmi ta kasa, wato NACOMYO, ta bayyana matsayrta game da tikitin Muslim Muslim na gwamnatin Bola Tinubu.

Kungiyar ta bayyana cewa sabanin zarge-zargen da ake yi, Kiristoci ne suka fi cin gajiyar gwamnatin Tinubu ta fuskar nade-naden mukamai da tallafin siyasa.

Musulmi suka ce Kiristoci sun fi cin moriyar gwamnatin Tinubu
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Kungiyar ta bayyana haka ne yayin mayar da martani kan sabuwar adawa da tsarin takarar Musulmi da Musulmi da ake sa ran jam’iyyar APC za ta sake amfani da shi a zaben shugaban kasa na shekarar 2027, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Rarara ya kira ruwa, PDP ta yi masa tatas kan taba Farfesa Pantami

Kiristoci sun yi adawa da tikitin Muslim/Muslim

A baya dai, kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) da National Christian Elders Forum (NCEF) da kuma Christian Youth Alliance of Nigeria (CYAN) sun nuna adawa da tsarin takarar Musulmi da Musulmi.

Sai dai NACOMYO ta bayyana wannan adawa a matsayin munafunci, tana mai cewa Kiristoci ne suka fi amfana da mukaman gwamnati fiye da sauran kungiyoyin addini.

A cikin sanarwar da sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Mas’ud Ayodele Akintola, ya sanya wa hannu, ya ce tun farkon gwamnatin Tinubu, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa kashi 62 cikin 100 na nade-naden mukamai an bai wa Kiristoci, yayin da sauran addinai suka samu kashi 38 cikin 100.

Akintola ya ce har yanzu wannan yanayi na ci gaba idan aka yi la’akari da maye gurbin tsohon ministan lantarki, Adebayo Adelabu, da kuma tsohon shugaban JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, da Kiristoci.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya nuna ɓacin ransa kan cin zarafin Musulmai yan ƙabilar Igbo

Ya kara da cewa Musulmi ne ya kamata su fi yin korafi idan aka duba abin da ya kira rashin daidaito a nade-naden mukaman gwamnati, cewar Daily Post.

An kare tikitin Musulmi da Musulmi na Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Bukatar kungiyar ga kungiyoyin addini a Najeriya

NACOMYO ta kuma yi kira ga kungiyoyin addini da su ci gaba da bai wa gwamnati shawara mai kyau da addu’o’i domin taimakawa kasar nan ta samu ci gaba maimakon yawan korafe-korafen da ba su da tushe.

Kungiyar ta kuma ambaci bayanin mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, cewa an ware naira miliyan 780 a kasafin kudinsa na 2026 domin tallafa wa majami’u 200 a mazabarsa ta Bende.

A cewar NACOMYO, babu wata kungiyar Musulunci da ta samu irin wannan kulawa a cikin kasafin kudin kasa, lamarin da kungiyar ta ce ya nuna cewa Kiristoci sun fi cin gajiyar tsare-tsaren gwamnati.

An kai korafin tiktin Muslim/Muslim ga Trump

Mun ba ku labarin cewa wasu kungiyoyin Kirista da masu rajin kare hakki daga jihohi 36 da Abuja sun aika wa Donald Trump da Majalisar Dokokin Amurka takarda.

Kungiyoyin sun ce ci gaba da tsayawa da tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2027 na iya kara tabarbarewar tsaron Kiristoci.

Kungiyar Christian Youth Alliance of Nigeria (CYAN) ta ce lakabin Country of Particular Concern (CPC) bai dakatar da kashe-kashen Kiristoci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.