Shari'o'i 6 da Suka Shafi INEC da Za Su Iya Sauya Yadda Za a Gudanar da Zaben 2027 a Najeriya

Shari'o'i 6 da Suka Shafi INEC da Za Su Iya Sauya Yadda Za a Gudanar da Zaben 2027 a Najeriya

FCT, Abuja - Kusan watanni hudu kenan bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar da sabon jadawalin shirye-shiryen babban zaben shekarar 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Sai dai, hukumar INEC ta tsinci kanta cikin jerin manyan shari'o'i da za su iya sauya yadda za a gudanar da zaben.

An shigar da INEC kararraki gaban kotu
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan na jawabi a wajen taro Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa a halin yanzu, akalla manyan shari'o'i shida da suka shafi INEC na gaban babbar kotun tarayya da kotun daukaka kara.

Ana kalubalantar hukumar INEC a kotu

Shari'o'in na kalubalantar ikon hukumar, sahihancin sabon jadawalin zabe da kuma matsayin wasu jam'iyyun siyasa a karkashin doka.

Ana sa ran hukuncin kotunan za su fayyace iyakar ikon gudanarwar INEC bisa dokar zabe tare da tantance jam'iyyun siyasar da za su samu damar shiga babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

Yayin da rikici ya barke a ADC, INEC ta kara wa'adin sa sunayen 'yan takara

Ga manyan shari'o'in da ke gaban kotuna:

1. Youth Party ta kalubalanci jadawalin INEC

Shari'ar nan SSSSSSSSSSSSSSSSSSSSSSSSSSSSSSSSita ce mai lamba FHC/ABJ/CS/517/2026, wadda jam'iyyar Youth Party ta shigar a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Jam'iyyar ta kalubalanci wasu muhimman sassan sabon jadawalin INEC, tana mai cewa hukumar ba ta da ikon doka na sanya wa'adin da zai rage lokutan da Dokar Zabe ta tanada.

A hukuncinta, babbar kotun tarayya ta bayyana cewa duk da INEC na da ikon gudanar da zabe da fitar da ka'idoji, ba za ta iya sauya ko rage wa'adin da dokar zabe ta tanada ba.

Saboda haka, kotun ta soke sassan jadawalin da suka ci karo da dokar zabe tare da hana INEC aiwatar da su, rahoton Premium Times ya nuna hakan.

Sai dai INEC ba ta gamsu da hukuncin ba, inda ta daukaka kara tana mai cewa kotun ta takaita mata ikon da kundin tsarin mulki da doka suka ba ta wajen tafiyar da harkokin zabe.

Kara karanta wannan

Rikicin ADC ya sauya salo a jihar Kano, lamari ya kai ga yan sanda

An riga an saurari karar a kotun daukaka kara, amma har yanzu ba a bayyana ranar yanke hukunci ba.

Ana kallon wannan shari'a a matsayin mai matukar muhimmanci saboda tana shafar wa'adin gudanar da zaben fidda gwani da kuma mika sunayen 'yan takara.

2. SDP ta kai INEC kara a kotu

Wata babbar shari'ar kuma ita ce mai lamba FHC/ABJ/CS/720/2026, wadda jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta shigar kan INEC.

Kamar yadda Youth Party ta yi, SDP ta kalubalanci wasu sassan sabon jadawalin zaben, musamman wadanda suka shafi gabatar da sunayen 'yan takara da maye gurbinsu.

Jam'iyyar ta ce wa'adin da INEC ta tsara ya saba wa dokar zabe, tare da neman kotu ta soke sassan da ake takaddama a kansu.

Kotun tarayya ta tabbatar da cewa INEC na da ikon tsara jadawalin zabe, amma ba ta da ikon sauya wa'adin da dokar zabe ta tanada kan gabatar da 'yan takara ko maye gurbinsu. Saboda haka kotun ta soke sassan jadawalin da suka sabawa dokar.

INEC ta sake daukaka kara, tana mai cewa kotun ba ta yi la'akari da hakikanin kalubalen gudanar da zabe ba, kuma dukkan matakan da ke cikin jadawalin an tsara su ne domin tabbatar da an gudanar da zabe cikin tsari.

Kara karanta wannan

Cuta ta barke a sansanin 'yan ta'addan ISWAP, mayaka da dama sun mutu a Borno

Kotun daukaka kara ta saurari karar tare da tanadar hukunci, inda ake zaman jiran abin da kotun za ta yanke.

3. Rikici kan jadawalin INEC

Daukaka karar da suka samo asali daga shari'o'in FHC/ABJ/CS/517/2026 da FHC/ABJ/CS/720/2026 sun zama daga cikin muhimman shari'o'in da suka fi daukar hankali kafin babban zaben 2027.

A daya daga cikin shari'o'in, babbar kotun tarayya ta ce INEC ta wuce iyakar ikon da doka ta ba ta lokacin da ta rage wa'adin da dokar zabe ta tanada a cikin sabon jadawalinta.

Ana sa ran hukuncin kotun daukaka kara zai fayyace iyakar ikon INEC wajen tsara wa'adin gudanar da ayyukan zabe da suka wuce abin da dokar zabe ta fayyace.

Ana kuma sa ran za a yanke hukuncin kafin a shiga matakin yakin neman zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Rahoton Businessday ya nuna cewa kotun daukaka kara ta tanadi hukuncinta a shari'o'ij da ke kalubalantar jawadalin zabe na INEC.

4. Shari'ar neman soke rajistar jam'iyyu 5

Wata muhimmiyar shari'a ita ce mai lamba FHC/ABJ/CS/2637/2026 wadda kungiyar Incorporated Trustees of the National Forum of Former Legislators ce ta shigar.

Kara karanta wannan

Za a zabi dalibai a jami'o'i 20 da suka yi fice a Najeriya a ba su kyautar kudi

Kungiyar ta shigar da karar ne kan hukumar zabe ta INEC da jam'iyyun ADC, Accord, Action Alliance (AA), Action People's Party (APP) da Zenith Labour Party (ZLP), cewar rahoton TheCable.

Babbar kotun tarayya ta amince da bukatar masu karar tare da umurtar INEC ta soke rajistar wadannan jam'iyyu biyar. Sai dai hukuncin bai fara aiki nan take ba.

Bayan jam'iyyun sun daukaka kara daban-daban, kotun daukaka kara ta dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an kammala sauraron daukaka karar.

Wannan mataki ya tabbatar da cewa jam'iyyun za su ci gaba da kasancewa a hukumance har sai an yanke hukunci na karshe.

5. An kalubalanci rajistar NDC

Wata shari'ar da ke gaban kotu ita ce mai lamba FHC/ABJ/CS/1115/2026. Ahidjo Ibrahim Karlahi ne ya shigar da karar kan INEC da jam'iyyar NDC.

Mai shigar da karar na kalubalantar matakin da INEC ta dauka wajen yi wa jam'iyyar NDC rajista da amincewa da ita, yana neman kotu ta tantance ko an bi kundin tsarin mulki da dokokin da suka dace.

Rahoton jaridar Thisday ya nuna cewa har yanzu shari'ar na gaban babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja.

Kara karanta wannan

NDC: Rikici kan zaɓen ƴan takara na ci gaba da rikita jam'iyyar su Kwankwaso

Ana shari'o'i da INEC a gaban kotu
Shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

6. ADC da Accord na neman a soke hukuncin kotu

Hukuncin babbar kotun tarayya kan shari'ar FHC/ABJ/CS/2637/2026 bai kawo karshen takaddamar ba.

Jam'iyyun ADC, Accord, Action Alliance, Action People's Party da Zenith Labour Party sun garzaya kotun daukaka kara domin neman a soke hukuncin da ya umurci INEC ta soke rajistarsu, rahoton Vanguard ya zo da labarin.

Hukumar INEC na daga cikin wadanda aka shigar da kara a daukaka karar. Jam'iyyun sun ce alkalin kotun farko ya yi kuskuren doka lokacin da ya ba da umarnin soke rajistarsu.

Hukuncin kotun daukaka kara zai tantance ko jam'iyyun biyar za su ci gaba da samun damar tsayar da 'yan takara kafin INEC ta fitar da jerin sunayen 'yan takarar shugaban kasa da na majalisar dokoki ta tarayya ranar 12 ga Satumban 2026 kamar yadda jadawalinta ya tanada.

Dalilin da ya sa shari'o'in suke da muhimmanci

Gaba daya, wadannan shari'o'i shida sun zama gwaji na farko da bangaren shari'a zai yi wa shirye-shiryen babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

Zargin badakalar Gbajabiamila: Jam'iyyar NDC ta mika bukata ga Tinubu da EFCC

Baya ga tantance halaccin sabon jadawalin INEC, kotuna za su kuma fayyace iyakar ikon hukumar bisa kundin tsarin mulki da kuma makomar wasu jam'iyyun siyasa a tsarin dimokuradiyyar Najeriya.

INEC ta hana tura sunayen 'yan takarar NNPP

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta hana jam'iyyar NNPP lambar shiga shafin shigar da bayanan 'yan takara.

Kusan dukkan jam'iyyun siyasa da aka yi wa rajista sun karbi lambobin shiga shafin daga hukumar INEC amma ban da NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng