An Shiga Tashin Hankali a Amurka, Mummunar Gobara Ta Tilasta Mutane Barin Gidajensu

An Shiga Tashin Hankali a Amurka, Mummunar Gobara Ta Tilasta Mutane Barin Gidajensu

  • Wata gobarar daji mai saurin yaɗuwa ta kusanci birnin Spokane da ke jihar Washington a kasar Amurka
  • An umarci dubban mazauna yankin su gaggauta barin gidajensu yayin da gobarar ta ƙara ƙarfi
  • Jihar Washington ta ayyana dokar ta-ɓaci saboda fari da gobarar daji da ta addabi mutane tare da tilasta su tserewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Amurka - Wata gobarar daji mai saurin yaɗuwa ta kusanci birnin Spokane da ke jihar Washington a ranar Asabar, lamarin da ya tilasta wa dubban mazauna yankin barin gidajensu.

Gwamnatin jihar Washington ta ayyana dokar ta-ɓaci sakamakon yadda gobarar daji ta ƙaru a lokacin da jihar ke fuskantar ɗaya daga cikin mafi munin lokutan gobara a tarihinta.

Gobara ta yi barna a Amurka
Wata gobarar daji da ta tashi a California Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Jaridar The Punch ta ce fiye da eka 200,000, kwatankwacin hekta 80,900, ne gobara ke ci a sassa daban-daban na jihar da ke arewa maso yammacin Amurka.

Kara karanta wannan

Sababbin bayanai sun fito kan zargin tsohon gwamna game da juyin mulkin Tinubu

Hakan na faruwa ne yayin da jihar ke fuskantar fari a shekara ta huɗu a jere, wanda ya zama mafi tsawon lokacin fari da aka taɓa samu a faɗin jihar.

Gwamna ya ayyana dokar ta-ɓaci

Gwamnan jihar Washington, Bob Ferguson, ya ce fari mai tsanani da iska mai ƙarfi sun haifar da yanayi mai haɗari a faɗin jihar.

“Farin da ya karya tarihi da kuma iska mai ƙarfi suna haifar da yanayi mai haɗari a faɗin jihar.” In ji shi

Gwamnan ya ƙara da cewa an haramta yawancin ayyukan kunna wuta a fili da kuma ƙona wasu abubuwa a gonaki har zuwa ƙarshen watan Satumba.

Shi ma kwamishinan filayen jama’a, Dave Upthegrove, ya ce shekarar ta kasance ɗaya daga cikin shekarun da aka fi fama da gobarar daji a tarihin jihar.

“Tuni wannan shekarar ta zama ɗaya daga cikin shekarun da muka fi fuskantar gobarar daji a tarihi, alhali mun fara watan Agusta ne kawai.” In ji shi

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan ƙarin kuɗin wutar lantarki a Najeriya

Gobara ta shiga birnin Spokane

Rahoton jaridar Spokesman-Review ya ce wata gobara da aka sanya wa suna Old Trails ta tsallaka kogin Spokane da yammacin ranar Asabar kafin ta shiga cikin birnin.

Hukumomi sun fitar da gargaɗin gaggawa mafi girma mai suna “Ku Tafi Yanzu”, inda aka umarci dubban mutane da ke wasu yankunan arewacin Spokane su bar gidajensu.

Bisa rahoton Spokesman-Review, gobarar ta mamaye fiye da eka 3,500 zuwa ƙarfe 8:20 na dare.

Jami’an birnin sun ce ba a samu rahoton wani da ya ji rauni ba.

Babban hafsan soji, Manjo Janar Gent Welsh, ya ce:

“Idan rana ta faɗi kuma ta sake fitowa, za mu shiga cikin firgici.”
Gobara ta yi gyara a Amurka
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An buɗe matsugunin gaggawa

Hukumomin bayar da agajin gaggawa sun buɗe wani matsuguni domin karɓar mutanen da aka kwashe daga gidajensu a Spokane Convention Centre.

Tun da farko a ranar Asabar, Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa ta fitar da gargaɗin Red Flag Alert kan wani yanayi da ta bayyana a matsayin mai matuƙar haɗari.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta lallaba Saudiyya, tana so a taimaka wa Najeriya kan karatun allo

Hukumar ta ce haɗarin yanayin ya kai matsayi mai tsanani a gabashin jihar Washington.

Rundunar tsaron ƙasa ta jihar Washington ta ce tana gaggauta tattara jami’anta domin taimaka wa birnin Spokane wajen shawo kan matsalar.

Gobara ta tashi a kasuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar sayar da kayan gida ta Kingsway da ke kan titin Murtala Muhammad Way a jihar Kano.

Gobarar wadda ta tashi cikin dare ta yi mummunar illa a shaguna tare kona kayayyaki masu dinbin yawa a kasuwar

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com