Gwamna Ya Ji Zazzafan Martani da Ya Tabo Kwankwaso, Obi a Kudancin Najeriya

Gwamna Ya Ji Zazzafan Martani da Ya Tabo Kwankwaso, Obi a Kudancin Najeriya

  • Kungiyar da ke goyon bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta ce ikirarin Gwamna Hope Uzodimma kan goyon bayan Bola Tinubu ba ra'ayin al'ummar Kudu maso Gabas ba ne
  • Ƙungiyar da ke kiran kanta Kwankwaso National Network ta ce za ta tattara aƙalla ƙuri'u miliyan biyar ga tikitin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a zaɓen 2027
  • Ta kuma yi gargaɗin cewa ka da a kuskura a maimaita matsalolin fasaha da aka fuskanta a zaɓen 2023 idan jama'a sun fita kada kuri'a a na 2027 mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Imo –Ƙungiyar Kwankwaso National Network (KNN) reshen Kudu maso Gabas ta yi watsi da ikirarin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma.

Gwamnan ya bugi kirji, ya yi ikirari cewa gwamnonin yankin sun amince da mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin sake lashe zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya kalubalanci Tinubu kan sayo motocin alfarma a kan N15.13bn

Kungiyar KNN ta ce Obi Kwankwaso za a yi a Kudu maso Gabas
Snata Rabi'u Musa Kwanwaso, Peter Obi Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta wallafa cewa amma a martaninta, shugaban KNN na shiyyar Kudu maso Gabas, Dakta Ukpai Ukpai, ya ce kalaman Uzodinma ra'ayinsa ba ne mutanen yankin ba.

Ukpai ya ce furucin da aka danganta da gwamnonin yankin ba ya nuna ra'ayin al'ummar Kudu maso Gabas, kuma ba ya ɗauke da amincewar masu kaɗa ƙuri'a na yankin.

Kungiyar Kwankwaso ta soki gwamnan Imo

A cewarsa, KNN tare da abokan hulɗarta sun ƙuduri aniyar samar da aƙalla ƙuri'u miliyan biyar daga jihohin Kudu maso Gabas domin tikitin haɗin gwiwar Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ya ƙara da cewa:

"A matsayinmu na ƙungiya mai ƙarfi da ke da ginshiƙi a matakin ƙasa a faɗin yankin, muna tunatar da shi cewa gwamnoni ba za su iya yanke wa yankin hukuncin zaɓin siyasa ba."

Har ila yau, ya yaba wa Kwankwaso bisa dakatar da burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa tare da amincewa da tikitin haɗin gwiwa da Obi.

Kara karanta wannan

Halin da Obi ya shiga da rikici ya danno cikin ƙungiyar tafiyarsa da Kwankwaso

KNN ta ce gwamnan Imo ya fadi ra'ayinsa ne game da Kwankwaso
Hope Uzodinma, gwamnan jihar Imo Hoto: Hope Uzodinma
Source: Twitter

Ya ce:

"Wannan mataki ne na dabaru domin kuɓutar da ƙasar nan daga ƙwacen siyasa da wasu tsirarun 'yan kasuwar siyasa suka yi, tare da haɗa kan ɓangarorin adawa da suka rabu."

Manufar kungiyar Kwankwasiyya

Ukpai ya bayyana cewa manufarsu ita ce tara aƙalla ƙuri'u miliyan ɗaya daga kowace jiha cikin jihohi biyar na yankin, domin su zarce sakamakon da Peter Obi ya samu a Kudu maso Gabas a zaɓen 2023.

Ya ce:

"Mun kuduri aniyar zarce abin da Peter Obi ya samu a 2023 a yankin, tare da tabbatar da cewa tikitin Obi da Kwankwaso ya samu gagarumar nasara a faɗin Kudu maso Gabas."

A cewarsa, ƙungiyar ta riga ta tanadi ingantattun dabaru domin cimma wannan buri, tare da samar da hanyoyin kare ƙuri'un al'umma.

Tikitin Obi, Kwankwaso ya samu karbuwa

A baya, mun wallafa cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya bayyana ra'ayinsa kan tikitin da zai iya lashe zaben shugaban kasa a babban zaben 2027 mai karatowa.

Kara karanta wannan

APC ta yi wa gwamnan Osun barazana ana dab da zabe

Babachir ya ce haɗakar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a takarar shugaban ƙasa za ta fi samun damar lashe zaɓen 2027 idan aka kwatanta da kowannensu ya tsaya shi kaɗai ba tare da taimakon dayan ba.

Ya yi hasashen cewa haɗakar Obi da Kwankwaso za ta samu kashi 70 cikin 100 na damar yin nasara, yayin da Shugaba Bola Tinubu zai samu kashi 50 cikin 100 yayin da yan Najeriya za su yi zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng