Abin da Yasa ba a Saki Muryar Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei ba har Yanzu

Abin da Yasa ba a Saki Muryar Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei ba har Yanzu

  • Wasu rahotanni sun bayyana dalilin da ya sa har yanzu hukumomi a Iran ba su fitar da muryar jagoran addini, Mojtaba Khamenei ba
  • Rahoton ya bayyana cewa masana na iya gano wuri, lokaci da na'urar da aka yi rikodi ta hanyar nazarin amo, wutar lantarki da sautin muhalli
  • Haka kuma fasahar tantance murya na iya gano wasu bayanai kan lafiyar mai magana, yanayin numfashinsa, bugun zuciya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Rahotanni sun bayyana dalilin da yasa ba a fitar da muryar jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei ba yayin da ake ci gaba da yaki.

Rahoto ya bayyana cewa har yanzu ba a fitar da rikodin sautin Khamenei na uku ga jama'a ba saboda dalilan tsaro da kuma ci gaban fasahar zamani ta binciken sauti.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya fadi yanayin da zai sa ya shiga daji ceto daliban da aka sace

Dalilin da yasa ba a sake muryar Mojtaba Khamenei ba
Jagoran addinin Musulunci a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Majiyoyi sun ce yanayin ɗakin da aka yi rikodi da yadda sauti ke dawowa daga bango na iya ba masana damar tantance girman ɗakin da kuma wasu siffofin wurin da aka yi rikodin, cewar BBC Hausa.

Musabbabin rashin sake muryar Mojtaba Khamenei

Haka kuma, nazarin mitar wutar lantarki da ake samu a cikin rikodin na iya taimaka wa masana wajen gano ainihin lokaci, ranar da kuma yankin da aka yi rikodin.

Rahoton ya ƙara da cewa fasahar nazarin sauti da kuma alamomin musamman na na'urar rikodi na iya taimakawa wajen gano irin makirufo ko na'urar da aka yi amfani da ita.

Amo daga injin sanyaya iska, janareta ko wasu na'urorin fasaha da ke cikin muhalli na iya ba da muhimman bayanai game da wurin da aka yi rikodin.

Akwai dalilin da ya sa ba a saki muryar Khamenei ba
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian a wurin taron kasa da kasa Hoto: Anadolu.
Source: Getty Images

Fargabar da ake yi game da tsaron Khamenei

Rahoton ya kuma bayyana cewa fasahar tantance murya na iya nazarin yanayin maganar mutum, numfashi, tsayawa tsakanin kalmomi da sauran siffofin murya domin gano wasu bayanai game da lafiyarsa.

Kara karanta wannan

ADC ta bukaci Tinubu ya ceto daliban Borno kamar na Oyo

Sai dai rahoton bai yi zargin cewa an gudanar da irin wannan bincike a kan Jagoran Kolin Iran na uku ba, illa ya yi bayanin irin damar da waɗannan fasahohi ke bayarwa da kuma dalilin da ya sa ake ɗaukar matakan tsaro wajen kare irin waɗannan rikodi.

Rahoton ya kuma bayyana cewa fasahar tantance murya na iya nazarin yanayin maganar mutum, numfashi, tsayawa tsakanin kalmomi da sauran siffofin murya domin gano wasu bayanai game da lafiyarsa.

Sai dai rahoton bai yi zargin cewa an gudanar da irin wannan bincike a kan Jagoran addini a Iran na uku ba, illa ya yi bayanin irin damar da waɗannan fasahohi ke bayarwa da kuma dalilin da ya sa ake ɗaukar matakan tsaro wajen kare irin waɗannan rikodi.

Mojtaba Khamenei ya gargadi Trump a sakon salla

Kun ji cewa yayin da sabon rikici ke son barkewa, Mojtaba Khamenei ya ce kasashen Gabas ta Tsakiya ba za su sake zama mafaka ga sansanonin sojin Amurka ba.

Tun bayan hawansa matsayin jagoran addini mafi girma na Iran, Mojtaba bai taba fitowa a bidiyo ko a gaban kyamara ba amma ya sha tura sakon gargadi.

A daya bangaren kuma, rundunar IRGC ta Iran ta ce ta harbo jirgin MQ-9 Reaper na Amurka, ta kuma harbi F-35 da jirgin leken asiri a sararin samaniyarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.