Saudiyya Ta Hango Babbar Matsala, Ta Kulla Sabuwar Alaka da Kasashen Afrika 5
- Saudiyya ta sanar da kafa sabon ƙawancen tsaron teku da ya haɗa ƙasashe takwas domin kare Tekun Bahar Maliya da Tekun Aden
- Ƙawancen ya haɗa da Masar, Sudan, Djibouti, Eritrea da Somalia, waɗanda ke da muhimman mashigai na ruwa a Afirka
- Saudiyya ta ce shirin zai kare hanyoyin kasuwanci da jigilar makamashi yayin da matsalolin tsaro ke ƙaruwa a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Saudiyya - Saudiyya ta sanar da shirin kafa wani sabon ƙawancen tsaron teku da ya haɗa ƙasashe takwas da ke bakin Tekun Bahar Maliya da Tekun Aden, domin ƙarfafa tsaro a ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin kasuwanci na duniya.
Ma'aikatar Tsaron Saudiyya ta bayyana cewa ƙawancen zai haɗa da Saudiyya, Jordan da Yemen, tare da ƙasashen Afirka guda biyar da suka haɗa da Masar, Sudan, Djibouti, Eritrea da Somalia.

Source: Twitter
Dalilin kafa sabon ƙawancen Saudiyya
A cikin wata sanarwa, ma'aikatar ta ce manufar ƙawancen ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen da ke bakin Tekun Bahar Maliya domin kare hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa na ƙasa da ƙasa, in ji rahoton Business Insider.
Ta ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da tsaron hanyoyin kasuwanci da jigilar makamashi, tare da bunƙasa haɗin gwiwa a fannin tsaron teku a Tekun Bahar Maliya, mashigar Bab el-Mandeb da Tekun Aden.
An bayyana cewa kusan kashi 12% na kasuwancin duniya ne ke bi ta wannan hanya, ciki har da jigilar man fetur, iskar gas (LNG) da kwantena tsakanin Turai, Asiya da Afirka.
Muhimman wannan ƙawancen
Sanarwar ta zo ne yayin da matsalolin tsaro ke ƙaruwa a yankin Bahar Maliya sakamakon hare-haren da aka riƙa kai wa jiragen kasuwanci, waɗanda ke da alaƙa da rikice-rikicen da suka shafi Amurka, Iran, Isra'ila da ƙungiyoyin da Iran ke goyon baya.
Saboda wannan matsala, kamfanonin jiragen ruwa da dama sun fara kauce wa Bahar Maliya, suna bi ta Cape of Good Hope, lamarin da ya ƙara kuɗin sufuri tare da jinkirta isar da kayayyaki zuwa kasuwannin Afirka da Turai.
Tasirin ƙawancen ga ƙasashen Afirka
Ga nahiyar Afirka, sabon ƙawancen ba wai na tsaro kaɗai ba ne, har ma yana da muhimmanci ga tattalin arziki, kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.
Masar, Djibouti, Eritrea da Somalia na daga cikin ƙasashen da ke da muhimman mashigan ruwa a nahiyar, yayin da Sudan ke da doguwar gabar Bahar Maliya da ke haɗa Arewaci da Gabashin Afirka.

Source: Getty Images
Mashigar Bab el-Mandeb da ke tsakanin Djibouti, Eritrea da Yemen na daga cikin wuraren da suka fi muhimmanci wajen zirga-zirgar jiragen ruwa a duniya.
Duk wani tangarɗa a wannan mashiga na iya shafar shigo da kaya, fitar da kayayyaki, samar da makamashi da kuma wadatar abinci a ƙasashen Afirka.
Haka kuma, Mashigar Suez ta Masar na ci gaba da kasancewa muhimmiyar hanyar kasuwancin duniya. Sai dai matsalolin tsaro a Bahar Maliya sun rage kuɗaɗen shiga da Masar ke samu daga mashigar, bayan da kamfanonin jiragen ruwa suka sauya hanyoyin zirga-zirgarsu domin kauce wa haɗarin yankin.

Kara karanta wannan
Minista ya cire tsoro, ya fadi babban abin da ke rura wutar ta'addanci a Najeriya
Saudiyya ta hana kasashe 3 shiga kasarta
A wani labari, mun ruwaito cewa, Saudiyya ta dakatar da shigar matafiya daga Dimokuraɗiyyar Kongo, Uganda da Sudan ta Kudu saboda matakan kariya daga Ebola.
Masu neman shiga Saudiyya da suka zauna a waɗannan ƙasashe cikin kwanaki 21 kafin tafiyarsu ma ba za a ba su biza ba.
Hukumar Weqaya ta tabbatar da cewa ba a samu wani tabbataccen ko wanda ake zargi da cutar Ebola a Saudiyya tun daga shekarar 2019 ba.
Asali: Legit.ng

