Tirkashi: An Saki Sunayen Kasashen Afrika 3 da Aka Hana Mutanensu Shiga Saudiyya
- Hukumomin Saudiyya sun dakatar da shigar matafiya daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Uganda da Sudan ta Kudu saboda matakan kariya daga Ebola
- Masu neman shiga Saudiyya da suka zauna a waɗannan ƙasashe cikin kwanaki 21 kafin tafiyarsu ma ba za a ba su biza ba
- Hukumar Weqaya ta tabbatar da cewa ba a samu wani tabbataccen ko wanda ake zargi da cutar Ebola a Saudiyya tun daga shekarar 2019 ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Saudiyya - Hukumomin Saudiyya sun sanar da dakatar da shigar matafiya daga ƙasashen Afirka uku a matsayin matakin kariya domin dakile yaduwar cutar Ebola, wadda ke ci gaba da barazana a wasu sassan nahiyar.
Hukumar Kula da Lafiyar Jama'a ta Saudiyya (Weqaya) ta bayyana cewa daga yanzu ba za a ba wa matafiya daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), Uganda da Sudan ta Kudu damar shiga ƙasar ba har sai an sake sanarwa.

Source: Getty Images
Saudiyya ta tsaurara matakan kariya
A cewar Weqaya, an kuma dakatar da bayar da kowane irin bizar shiga Saudiyya ga mutanen da suka zauna a ɗaya daga cikin waɗannan ƙasashe cikin kwanaki 21 kafin tafiyarsu, ko da kuwa sun bi ta wata ƙasa kafin su isa Saudiyya, in ji rahoton Arab News.
Hakazalika, hukumomin Saudiyya sun ƙarfafa matakan binciken lafiya ga matafiya da ke shigowa daga Rwanda, Burundi, Tanzaniya da Jamhuriyar Kongo (Congo-Brazzaville).
Za a riƙa gudanar da gwajin lafiya da sa ido kan alamun cutar ga matafiya daga waɗannan ƙasashe a mashigun ƙasar.
Ba a samu Ebola a Saudiyya ba
Hukumar Weqaya ta tabbatar da cewa ba a samu wani tabbataccen ko wanda ake zargi da cutar Ebola a Saudiyya ba tun bayan shekarar 2019.
Ta ce tsarin sa ido da dakile haɗarin cututtuka na ci gaba da aiki ba dare ba rana tare da haɗin gwiwar hukumomin cikin gida da na ƙasa da ƙasa domin kare lafiyar 'yan ƙasa, mazauna ƙasar da baƙi.
An wallafa a shafin gwamnatin Saudiyya cewa hukumar ta jaddada cewa sabbin matakan kariyar na rigakafi ne kawai, kuma an ɗauke su ne domin hana shigowar cutar cikin ƙasar.
Cutar Ebola ta yi ajalin dubban mutane
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an fara gano cutar Ebola ne a shekarar 1976 a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Tun daga lokacin, cutar ta yi sanadin mutuwar kusan mutum 15,000, yayin da kusan rabin waɗanda ke kamuwa da ita ke rasa rayukansu.

Source: Getty Images
A ranar Laraba, hukumomin Faransa sun tabbatar da bullar cutar Ebola ta farko a ƙasar bayan wani likita da ya dawo daga aikin jin ƙai a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya kamu da cutar.
An kwantar da likitan a wani cibiyar killace masu ɗauke da cututtuka masu haɗari, yayin da hukumomin lafiya ke ci gaba da sa ido kan lamarin.
Weqaya ta ce za ta ci gaba da bibiyar yadda cutar ke yaɗuwa a yanki da ma duniya baki ɗaya tare da haɗin gwiwar hukumomin lafiya domin tabbatar da tsaron lafiyar al'umma.
Saudiya ta yi magana da Trump
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya ce ƙawayensu a Gabas ta Tsakiya sun cimma muhimman sharuɗɗan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Iran.
Ya bayyana cewa yarjejeniyar za ta haɗa da buɗe mashigin Hormuz gaba ɗaya, tare da dakile barazanar shirin nukiliyar Iran idan an cimma matsaya.
Isra'ila ta amince da haɗa kai da Amurka wajen kammala yarjejeniya, amma Iran ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan ikirarin Trump ba.
Asali: Legit.ng


