NDC: Rikici kan Zaɓen Ƴan Takara na Ci gaba da Rikita Jam'iyyar Su Kwankwaso
- 'Yan jam'iyyar NDC da ke Kudu maso Gabas sun yi gargadin cewa akwai matsala gagaruma idan aka ci gaba da kakaba masu 'yan takara
- 'Yan jam'iyyar da suka yi magana da murya daya sun ce jinkirin fitar da sakamakon zaɓen fitar da gwani na iya haifar da sabon rikici kafin zaɓen 2027
- Ƙungiyar yankin Kudu maso Gabas ta bukaci a mutunta dimokuraɗiyyar cikin gida tare da miƙa sunayen waɗanda suka yi nasara a sahihin zaɓe ga INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa
FCT Abuja - Ƙungiyar yankin Kudu maso Gabas ta jam'iyyar NDC ta yi kira ga shugabannin jam'iyyar na ƙasa da su guji jinkirta fitar da sakamakon zaɓen fitar da gwani da kuma kakaba 'yan takara.
'Kungiyar ta yi gargadin cewa irin wannan mataki na iya haddasa sabon rikicin cikin gida tare da raunana jam'iyyar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gargaɗin na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyun siyasa ke ƙoƙarin cika wa'adin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gindaya na miƙa sunayen 'yan takararsu domin zaɓen 2027.
Yan NDC sun fusata
Jaridar Punch ta wallafa cewa da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Lahadi, 5 ga watan Yuli, 2026 shugaban NDC na yankin Kudu maso Gabas a Babban Birnin Tarayya (FCT), Maxwell Igbokwe, ya ce a yi gyara.
Ya buƙaci shugabancin jam'iyyar ya mutunta dimokuraɗiyyar cikin gida tare da tabbatar da cewa waɗanda suka samu nasara ta hanyar sahihin zaɓen fitar da gwani ne kawai za a tura sunayensu ga INEC.
MaxwellIgbokwe ya bayyana damuwarsa kan yadda har yanzu ba a sanar da sakamakon wasu zaɓukan fitar da gwani da aka gudanar fiye da watanni biyu da suka gabata ba.
Igbokwe ya ce:
"Muna kira ga shugabannin jam'iyyarmu da su mutunta kundin tsarin mulkin NDC, su girmama sakamakon zaɓen fitar da gwani na gaskiya da bin doka, tare da tabbatar da cewa ba a kakaba wa jama'a wani ɗan takara ba."
Yan NDC sun shiga damuwa
Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa an yi magudi a zaɓen fitar da gwani na kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar AMAC/Bwari a Abuja.
A cewarta, an kafa NDC ne domin kawo sabon salo na dimokuraɗiyya da gaskiya, sabanin abin da ake zargin tsofaffin jam'iyyun siyasa da aikatawa, don haka bai kamata jam'iyyar ta kauce wa manufofinta ba.
Ya ƙara da cewa binciken da suka gudanar ya nuna akwai alamun yunƙurin maye gurbin wanda ya yi nasara ko kuma kakaba wani ɗan takara ba tare da bin tsarin dimokuraɗiyya ba.
A cewarsa, idan aka bari hakan ta faru, zai lalata martabar NDC tare da karya ƙa'idodin adalci da bin doka da aka kafa jam'iyyar a kansu.
Ganduje ya magantu kan shiga NDC
A baya mun wallafa cewa tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi martani ga jita-jita da ta fara karfi cewa yana shirin rabuwa da jam'iyya mai mulki domin hade wa da 'yan adawa.
Rahotanni daga jihar Kano sun yi zargin cewa akwai alamu masu karfi na cewa Ganduje zai iya hade wa da tsohon mai gidansa, Rabiu'u Musa Kwankwaso a jam'iyyar NDC da ke adawa da Bola Tinubu.
Sai dai Ganduje bai yi shiru ba, ya bayyana cewa ba shi da ra'ayin barin jam'iyyarsa saboda bukatar kashin kai kamar yadda wasu 'yan siyasa ke yi idan suka gaza cimma manufarsu.
Asali: Legit.ng


