Mummunar Gobara Ta Tashi a Babban Filin Jirgin Saman Najeriya
- Hukumar FAAN ta tabbatar da tashin gobara a Terminal 2 na filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas ranar Lahadi
- Hukumar ta ce jami'an kashe gobara sun gaggauta isa wurin domin dakile yaɗuwar wutar, tare da tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba
- Gobarar ta taso ne watanni bayan wata irin ta lalata muhimman na'urorin sadarwa a Terminal 1 na filin jirgin saman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Legas - An samu tashin gobara a ranar Lahadi a Terminal 2 na Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas, lamarin da ya sa hukumomin kula da filayen jiragen sama suka gaggauta ɗaukar matakin gaggawa.
Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa, tana mai cewa jami'anta na kashe gobara sun isa wurin cikin gaggawa domin shawo kan lamarin.

Source: Getty Images
FAAN ta yi bayani kan gobara
A cewar FAAN, jami'an sashen kashe gobara na filin jirgin sama (ARFFS) sun fara aiki nan take domin hana wutar yaɗuwa zuwa sauran sassan tashar, in ji rahoton Channels TV.
Hukumar FAAN ta ce jami'an ceto da kashe gobara sun ci gaba da aiki domin kare lafiyar fasinjoji, ma'aikata da kuma kayayyakin da ke cikin Terminal 2.
FAAN ta kuma tabbatar da cewa zuwa lokacin fitar da sanarwar, ba a samu rahoton mutuwa ko jikkata sakamakon gobarar ba.
Ta ƙara da cewa ana ci gaba da sa ido kan lamarin, yayin da ake ƙoƙarin shawo kansa gaba ɗaya.
Ba a gano musabbabin gobarar ba
Hukumar ta ce har yanzu ba a bayyana musabbabin tashin gobarar ba, amma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano abin da ya haddasa lamarin.
FAAN ta ce za ta fitar da ƙarin bayani yayin da ayyukan kashe gobarar da bincike ke ci gaba.
Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed shi ne mafi yawan zirga-zirga a Najeriya, inda dubban fasinjoji ke amfani da shi a kullum domin zirga-zirgar cikin gida da ta ƙasashen waje.
Gobara ta taɓa afkuwa a filin jirgin
SaharaReporters ta ruwaito cewa wannan ba shi ne karon farko da ake samun tashin gobara a filin jirgin ba.
A watan Fabrairun wannan shekarar, wata gobara da ta tashi a Terminal 1 ta lalata muhimman na'urorin sadarwa tsakanin jiragen sama da Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA).

Source: Facebook
Lamarin ya tilasta wa masu kula da zirga-zirgar jiragen sama amfani da na'urorin ajiyar gaggawa domin ci gaba da gudanar da ayyuka, yayin da aka dakatar da saukar wasu jiragen sama na ɗan lokaci.
Hakazalika, a watan Satumban 2023, an samu hayaƙi a sashen jiragen ƙasa da ƙasa na Terminal 1, inda FAAN ta ce ana zargin wata matsalar lantarki ce ta haddasa lamarin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomi ba su bayyana musabbabin gobarar da ta tashi a Terminal 2 ba, yayin da jami'an agajin gaggawa ke ci gaba da ƙoƙarin kashe wutar da tabbatar da tsaron filin jirgin.
Gobara a filin jirgin saman Legas
A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar FAAN ta tabbatar da tashin gobara a wani sashen filin jirgin sama na Muratala Muhammed da ke jihar Legas.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta kama a wani bangaren da ake yi wa gyara domin sabunta shi da nufin inganta walwalar fasinjoji.
FAAN ta kwantar da hankulan fasinjoji da ke kai komo a filin jirgin, inda ta ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon gobarar.
Asali: Legit.ng


