Hankula Sun Tashi da 'Yan Bindiga Suka Babbake Mutane a Wani Sabon Harin Ta'addanci

Hankula Sun Tashi da 'Yan Bindiga Suka Babbake Mutane a Wani Sabon Harin Ta'addanci

  • Ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Lajinge da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto, inda suka kashe mutum 12
  • An ce mutum shida daga cikin waɗanda suka mutu sun ƙone da ransu bayan maharan sun banka wa ɗakin da suka fake wuta
  • Mazauna ƙauyen sun ce harin ya ɗauki kusan sa’o’i huɗu ba tare da jami’an tsaro sun kawo musu ɗauki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Sokoto - Akalla mutum 12 ne suka mutu, ciki har da shida da aka ƙona da ransu, bayan wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari a jihar Sokoto.

'Yan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Lajinge da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

'Yan bindiga sun yi barna a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa maharan sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 11:00 na dare ranar Asabar, 1 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Tashin hankali da 'yan bindiga suka kashe sojoji da sace mutane a Zamfara

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Sokoto

'Yan bindigan sun ci gaba da kai hari har zuwa wajen ƙarfe 3:30 na asubahin ranar Lahadi, 2 ga watan Agustan 2026 ba tare da wani ɗauki daga jami’an tsaro ba.

Wani mazaunin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mutum 11 daga cikin waɗanda suka mutu sun samu raunukan harbin bindiga, yayin da wata mata mai suna Agada ta mutu sakamakon tsananin firgici da ta shiga yayin harin.

A cewarsa, mutum shida sun ƙone da ransu bayan ƴan bindigar sun kewaye wani ɗaki da suka shiga suka fake.

“Sun umarci waɗanda ke cikin ɗakin su fito, amma suka ƙi. Daga nan sai maharan suka zuba fetur a ɗakin tare da harba bindiga. Lokacin da waɗanda ke ciki suka yi ƙoƙarin fita ta ƙofar ɗakin, sai suka ci gaba da harbinsu. An bar gawarwakinsu a cikin ɗakin da ke ci da wuta.” In ji shi

Kara karanta wannan

Jirgin sama ya yi mummunan hatsari, dukkan fasinjojin da ya dauko sun mutu

An ƙone wasu da ransu

Majiyar ta bayyana sunayen waɗanda suka mutu a gobarar da suka haɗa da mai gidan, Malam Wauro, wanda aka fi sani da Malam Roro, da ’ya’yansa maza biyu, Ukasha da Mujaheed.

Sauran sun haɗa da wasu danginsa biyu da aka bayyana sunayensu a matsayin Sufyanu da Sani Shanbami, da kuma wani mutum da ya rasa matsuguninsa sakamakon rikici wanda ya nemi mafaka a gidan.

Majiyar ta ƙara da cewa wani mutum mai suna Lawwali ya mutu bayan an harbe shi a bakin ƙofar gidan yayin da yake ƙoƙarin tserewa. Hakan ya sa adadin waɗanda suka mutu a gidan ya kai mutum bakwai.

Yadda maharan suka kai hari

Wani mazaunin ƙauyen da ya shiga aikin sintiri tare da ƴan banga a daren da aka kai harin ya ce suna tsaye kusa da makarantar firamare ta ƙauyen lokacin da ƴan bindigar suka kai farmaki.

“Muna wajen makarantar firamare muna gadin ƙauyen sai muka ji ƙarar harbe-harbe masu ƙarfi ba zato ba tsammani. Dukkanmu muka ruga domin neman mafaka, kuma muna ta sauya wuraren ɓuya duk lokacin da harbin ya matsa kusa da mu.” In ji shi

Kara karanta wannan

INEC ta cire sunayen ƴan takara, an cire sunan Jonathan, Goje da manyan ƴan siyasa

Ya ce bayan maharan sun rinjayi ƴan banga, sai suka riƙa yawo cikin ƙauyen ba tare da wata matsala ba, suna shiga gida-gida tare da kwashe shanu da tumaki.

Ya ƙara da cewa daga baya maharan sun nufi wani ɓangaren ƙauyen, inda suka kai hari gidan Malam Wauro.

An ce sun kashe Malam Wauro da ’ya’yansa maza biyu, tare da yin garkuwa da matansa biyu da kuma kwashe dukkan shanunsa.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu Sokoto Hoto: Ahmad Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, inda ya ce bai samu labarin harin ba.

Kakakin 'yan sandan ya ce yana kan hanya kuma zai binciki lamarin da zarar ya isa ofishinsa. Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, bai sake bayar da wani bayani ba.

'Yan bindiga sun kashe babban soja

A wani labarin kuma, kun ji cewa yan bindiga dauke da makamai sun kashe Kanal Abdussalam Ude, wani jami’i mai aiki a rundunar sojojin Najeriya a Abuja.

'Yan bindigan sun kuma harbi matarsa a gidansu da ke yankin Kurudu na babban birnin tarayya, Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng