Za a Zabi Dalibai a Jami'o'i 20 da Suka Yi Fice a Najeriya a Ba Su Kyautar Kudi

Za a Zabi Dalibai a Jami'o'i 20 da Suka Yi Fice a Najeriya a Ba Su Kyautar Kudi

  • Kamfanin Stransact zai karrama dalibai 100 mafi hazaka daga manyan jami'o'i 20 na Najeriya saboda bajintar da suka nuna
  • Dukkan dalibin da aka zaba zai samu N100,000, takardar karramawa da kuma damar shiga shirin bunkasa rayuwar dalibai
  • Biyo bayan lamarin, shugabannin jami'o'i sun yaba da shirin da kamfanin ya kawo, suna cewa zai karfafa hazakar 'yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanin Stransact ya sanar da shirin ba dalibai 100 da suka nuna bajinta yayin kammala karatu daga jami'o'i 20 mafi daraja na Najeriya kyaututtuka karkashin shirin Stransact Honours Roll.

Ya bayyana cewa an kirkiro shirin ne domin karfafa hazaka a fannin karatu tare da shirya matasa domin fuskantar kalubalen rayuwar yau.

Jami'ar ABU da ke Zaria, jihar Kaduna.
Ginin da ke kofar shiga jami'ar ABU Zaria. Hoto: Ahmadu Bello University Zaria
Source: Facebook

Daliban jami'o'in da za a zaba

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka fatattaki 'yan ta'adda da suka kai hari sansanin sojojin Zamfara

Vanguard ta wallafa cewa shirin zai karrama dalibai biyar mafi hazaka daga kowace jami'a cikin jami'o'in da suka shiga jerin jami'o'i masu hazaka na THE na 2026.

Kowanne daga cikin wadanda za a zaba zai samu kyautar kudi N100,000, takardar karramawa ta kamfanin, da kuma shiga kai tsaye cikin shirin bunkasa wadanda suka kammala karatu na kamfanin.

Jami'o'in da ke cikin shirin sun hada da:

  1. Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya
  2. Jami'ar Afe Babalola
  3. Jami'ar Babcock
  4. Jami'ar Bayero da ke Kano
  5. Jami'ar Covenant
  6. Jami'ar Jihar Delta
  7. Jami'ar Jihar Ekiti
  8. Jami'ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure
  9. Jami'ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri
  10. Jami'ar Jihar Legas
  11. Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola
  12. Jami'ar Obafemi Awolowo
  13. Jami'ar Benin
  14. Jami'ar Ibadan
  15. Jami'ar Jos
  16. Jami'ar Legas
  17. Jami'ar Ilorin
  18. Jami'ar Uyo
  19. Jami'ar Nnamdi Azikiwe
  20. Jami'ar Najeriya da ke Nsukka

Martanin shugabannin jami'o'i

Business Day ta wallafa cewa shugabannin jami'o'in sun yaba da wannan shiri, inda suka ce shirin zai karrama dalibai da kuma karfafa alakar jami'o'i da bangaren masana'antu.

Sun ce irin wannan karramawa za ta kara zaburar da dalibai wajen yin kokari a karatu tare da taimakawa wajen samar da kwararrun ma'aikata da ake bukata domin ci gaban kasa.

Kara karanta wannan

Zargin badakalar Gbajabiamila: Jam'iyyar NDC ta mika bukata ga Tinubu da EFCC

Shugaban Jami'ar Ilorin, Farfesa Wahab Egbewole, ya bayyana shirin a matsayin abin yabawa, yana mai cewa hakan zai karfafa gwiwar dalibai wajen neman ilimi da bayar da gudunmawa ga al'umma.

Dalibai na fita daga jami'ar Legas
Yadda ake fita daga jami'ar Legas bayan tarzomar dalibai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya kuma yi maraba da kasancewar Jami'ar Ilorin cikin jami'o'i 20 na Najeriya, yana mai cewa hakan zai kara zaburar da jami'ar wajen ci gaba da kokari a fannonin koyarwa, bincike, kirkire-kirkire da hidimar al'umma.

An takaita ibada a jami'ar ATBU

A wani labarin, mun kawo muku cewa hukumar gudanarwar jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi ta takaita gudanar da ibada a masallatan makarantar.

Hakan na zuwa ne bayan sabanin da aka samu game da warewa wasu 'yan Darikar Tijjaniyya masallacin da suka kebanta da shi a jami'ar.

A yanzu haka, kakakin jami'ar, Malam Zailani Bappah ya sanar da cewa salloli biyar da Juma'a za a rika yi har sai an shawo kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng