Shugaban INEC Ya Fallasa babbar matsala a rajistar masu zaɓe
- Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ya bayyana kalubalen da ya dabaibaye rajistar zabe gabanin kada kuri'a a 2027 mai zuwa
- Farfesa Joash Amupitan ya ce rashin sabunta rajistar tun daga 2011 ya sa ana ci gaba da samun matsaloli a cikin sunayen masu kada kuri'a
- Hukumar zabe ta INEC ta nemi haɗin gwiwar Hukumar wayar da kan jama'a, NOA wajen wayar da kan jama'a gabaninbabban zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa rajistar masu kaɗa ƙuri'a da hukumar ke amfani da ita har yanzu tana ɗauke da sunayen mutanen da suka rasu.
Rajistar, wacce aka yi amfani da ita a babban zaɓen shekarar 2023, na ɗauke da sunayen sama da mutum miliyan 93 da suka shigar da bayanansu a wancan lokaci.

Source: Facebook
The Nation ta wallafa cewa tun bayan wannan lokaci, INEC ta ci gaba da yin rajistar masu zaɓe, daga ciki har da wadda ake yi yanzu da za ta ƙare ranar 10 ga Yulin 2026, inda ake sa ran za a ƙara kusan mutum miliyan uku.
Akwai kalubale a rajistar zabe -INEC
Joash Amupitan ya ce rajistar da aka fara tattarawa tun shekarar 2011 ba a taɓa yin cikakken bita a kanta ba, duk da cewa mutane da dama sun rasu ko kuma sun yi ƙaura zuwa wasu ƙasashe.
A cewarsa:
"Za ku tuna da wasu daga cikin 'yan uwanku da suka rasu amma har yanzu sunayensu na cikin rajistar masu zaɓe, kuma ana ƙididdige su wajen tantance yawan masu fitowa zaɓe."
Ya ƙara da cewa kafin amfani da fasahar zamani wajen rajistar masu zaɓe, mutane na iya rubuta sunaye da dama ba tare da tantancewa ba.
"Kafin shekarar 2011, lokacin da ba a amfani da tsarin dijital, mutum zai iya rubuta sunaye 50 kawai ya kawo a yi rajista. Wasu daga cikin sunayen ba na mutane na gaske ba ne, amma har yanzu suna cikin rajistar."
Zabe: INEC ta nemu taimakon NOA
Shugaban hukumar INEC ya ce hanya mafi dacewa wajen tsaftace rajistar ita ce tsarin ƙorafi da ƙalubale, amma ya nuna damuwa cewa jama'a ba sa kai rahoton mutanen da suka rasu ko suka bar unguwanninsu.

Source: Facebook
Ya ce:
"Abin da za mu iya yi shi ne tsarin ƙorafi da ƙalubale. Amma mutane ba sa fitowa a rumfunan zaɓensu su ce wannan mutum ya rasu ko kuma ya daina zama a wannan al'umma."
Joash Amupitan ya kuma nemi NOA ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan 'yan Najeriya game da haƙƙinsu da alhakinsu na zaɓe.
INEC na shirin zamantar da katin zabe
A wani labarin mun wallafa cewa hukumar INEC ta sanar da cewa yanzu mutum zai iya sauke katin zaben shin a PVC da kansa, a maimakon sai ya je ofishin hukuma da ke kusa da shi domin ya karba hannu da hannu.
Shugaban hukumar zaben, Farfesa Joash Amupitan ya yi bayanin kokarin da ake yi na ganin mutane sun iya yin rajistar PVC ba tare da ziyartar ofishin INEC ba wanda zai kara saukaka al'amuran zabe a kasar nan.
Amupitan ya kara da cewa hukumar INEC za ta fara bayar da damar sauke sabon PVC ne ga wanda katinsu ya bace ko ya lalace daga zaben gwamnan jihar Osun da ake shirin gudanarwa.
Asali: Legit.ng

