NNPP Ta Gamu da Matsala, INEC Ta Hana Ta Tura Sunayen 'Yan Takararta na Zaben 2027
- Hukumar INEC ta hana jam'iyyar NNPP damar tura sunayen 'yan takararta a shafin yanar gizo yayin da shirye-shiryan zaben 2027 ke kara kankama
- Bayanai sun nuna cewa har zuwa yammacin ranar Talata, 30 ga watan Yuni, 2026, NNPP ba ta karbi lambar daga INEC ba
- Wani jami'in INEC ya tabbatar da cewa an bai wa kusan duka jam'iyyun siyasa lambobin shiga shafin amma ban da NNPP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bai wa kusan dukkan jam'iyyun siyasa da aka yi wa rajista lambobin shiga shafin tura sunayen 'yan takararsu a zaben 2026.
To sai dai bayanai sun nuna cewa INEC ta hana jam'iyyar NNPP lambar shiga shafin shigar da bayanan 'yan takara har zuwa yammacin jiya Talata, 30 ga watan Yuni, 2026.

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa duk sauran jam'iyyun siyasa, ciki har da jam'iyyar NDC, sun riga sun karbi lambobin shiga duk da hukuncin kotun da ya shafi jam'iyyar.
INEC ta karɓi daukaka karar NDC
Wani babban jami'in INEC ya bayyana cewa hukumar ta bai wa NDC damar shiga shafin ne bayan ta yi la'akari da cewa jam'iyyar ta daukaka kara kan hukuncin kotu tare da neman dakatar da aiwatar da hukuncin.
Jami'in ya kara da cewa kasancewar karar tana gaban kotu tare da bukatar dakatar da aiwatar da hukuncin ya isa dalilin da ya sa ba za a hana NDC damar amfani da shafin tantance 'yan takara ba.
NNPP ba ta karbi lambobin INEC ba
Ya kuma bayyana cewa zuwa yammacin Talata, kusan dukkan jam'iyyun siyasa da aka yi wa rajista sun karbi lambobin shiga shafin daga hukumar INEC amma ban NNPP.
Sai dai bai bayyana dalilin hana jam'iyyar NNPP damar shigar da yan takararta a shafin INEC ba, amma ana ganin hakan ba zai rasa nasaba da rigingimun cikin gida da take fama da shi ba.

Kara karanta wannan
NDC ta ɗauki mataki bayan hukuncin kotu, ta fara tura sunayen 'yan takara ga INEC
"Na tabbatar cewa dukkan jam'iyyu sun karbi lambobinsu ban da NNPP," in ji jami'in INEC.
Mene ne amfanin lambar shiga?
Lambar shiga da INEC ke bai wa jam'iyyun siyasa na ba su damar shigar da bayanan 'yan takararsu a Dandalin Tantance 'Yan Takara na Hukumar Zabe (ICNP), bisa jadawalin shirye-shiryen zabukan da hukumar ta fitar.

Source: Twitter
Matakin ya biyo bayan muhawarar da ta taso kan dalilin da ya sa INEC ta bai wa NDC damar shiga shafin duk da hukuncin kotu da ya shafi jam'iyyar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Sai dai hukumar ta jaddada cewa bai wa NDC lambar shiga ba ya nufin ta yanke hukunci kan shari'ar da ke gaban kotu, domin za ta mutunta duk hukuncin da kotu za ta yanke a karshe.
Jam'iyyu 9 sun karbi lambobin INEC
A wani rahoton, kun ji cewa INEC ta ce jam’iyyun siyasa tara sun karɓi lambobin shiga domin shigar da bayanan ‘yan takarar shugaban kasa da ‘yan majalisa na 2027.
Kwamishinan INEC mai kula da wayar da kan masu zabe da hulɗa da jama’a, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja.
Haruna ya ce hukumar ta fitar da ka’idojin gabatar da sunayen ‘yan takara, inda ya shawarci jam’iyyun siyasa su bi dokokin da aka gindaya.
Asali: Legit.ng
