Yadda Atiku, Tinubu da Obi Suka Ki Dora Wasu Muhimman Takardunsu a Shafin INEC

Yadda Atiku, Tinubu da Obi Suka Ki Dora Wasu Muhimman Takardunsu a Shafin INEC

  • Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa bayanan ‘yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a zaɓen 2027
  • Bayanai sun haɗa da cikakkun sunaye, jinsi, adireshin zama, matakin ilimi da tarihin aiki na 'yan takarar
  • Takardun sun nuna bambanci a bayanan ilimin Bola Tinubu, Peter Obi, Atiku Abubakar da Omoyele Sowore

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

FCT, Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa bayanan ‘yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa da za su fafata a zaɓen 2027.

An sanya bayanan a ofisoshin hukumar da ke hedikwatar ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar nan. Hukumar ta kuma wallafa bayanan ‘yan takarar mataimakin shugaban ƙasa.

INEC ta fitar da bayanan karatun Tinubu, Obi da Atiku
Peter Obi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Mr. Peter Obi, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce takardun sun ƙunshi cikakkun sunayen ‘yan takara, jinsinsu, adireshin wuraren zamansu, takardun shaidar karatu da kuma tarihin ayyukansu.

Kara karanta wannan

Komai ya fito fili, INEC ta saki bayanan karatun Tinubu da Shettima

INEC ta ce sashe na 29 (3) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya tanadi wallafa bayanan ‘yan takara cikin kwanaki 21 bayan karɓarsu.

Wane takardu Tinubu ya mika?

A cikin bayanan da INEC ta wallafa, Tinubu bai bayar da cikakkun bayanai kan makarantun firamare da sakandaren da ya halarta ba.

Ya bayyana takardar shaidar jami’a kaɗai, inda ya nuna cewa ya samu digirin BSc a shekarar 1979.

Haka kuma, an haɗa takardar shaidar karatunsa ta Chicago State University (CSU) cikin takardun.

Takardar shaidar Tinubu daga CSU ta jawo ce-ce-ku-ce sosai kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

A lokacin zaɓen 2023, an yi zargin cewa Bola Tinubu da ya halarci CSU ba shi ne shugaban Najeriya na yanzu ba.

Kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Tinubu bai bayar da bayanan makarantun firamare da sakandaren da ya halarta ba a cikin takardun da ya miƙa wa INEC.

Bayanai kan karatun Peter Obi

Kara karanta wannan

Zargin almundahanar kudi: An fara shirin tsige kakakin majalisa a Najeriya

Saɓanin Tinubu, Obi ya bayyana dukkan matakan karatunsa, ciki har da makarantun firamare da sakandaren da ya halarta da kuma jami’a.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce ya kammala karatun firamare a Augustine’s Primary School da ke Anambra a shekarar 1973.

Ya kuma ce ya kammala karatun sakandare a Christ the King College a shekarar 1978.

An haɗa takardun shaidar karatunsa na firamare da sakandare cikin bayanan da ya miƙa wa INEC.

Obi ya bayyana University of Nigeria, Nsukka (UNN) a matsayin jami’ar da ya yi karatu, inda ya nuna cewa ya kammala a shekarar 1984 tare da haɗa takardar shaidarsa.

Abin da Atiku ya bayyana

Bayanan Atiku sun nuna cewa ya samu takardar shaidar kammala firamare (FSLC) a shekarar 1954 da takardar shaidar West African School Certificate a shekarar 1961.

Sai dai bai bayyana makarantun da ya halarta ba, kuma bai haɗa takardun shaidar karatun guda biyu ba.

Amma ya haɗa takardar shaidar digirinsa na MA a fannin hulɗar ƙasashen duniya, wanda ya samu daga Anglia Ruskin University da ke Ingila a shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Duk da rashin tabbas kan makomarta, tsagin PDP ya mika sunan Jonathan ga INEC

Bayanan karatun Sowore

Omoyele Sowore, ɗan takarar shugaban ƙasa na African Action Congress (AAC), ya bayyana cewa ya samu takardar shaidar kammala firamare a shekarar 1980.

Ya kuma ce ya samu takardar shaidar West African Examinations Council (WAEC) a shekarar 1987 da kuma digirin MA a shekarar 2003.

Atiku zai yi takara a 2027
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taron jam'iyyar NDC Hoto: @atiku
Source: Twitter

Sai dai Sowore bai bayyana makarantun firamare da sakandaren da ya halarta ba. Haka kuma, bai bayyana ko ya samu digirin farko ba a cikin bayanan da ya miƙa wa INEC.

Sai dai ya haɗa hujjar takardar shaidar digirinsa na MA da ya samu daga Columbia University.

Sakon Atiku ga matasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a zaben 2027, Atiku Abubakar ya ba matasa shawara.

Atiku ya buƙaci matasan Najeriya da kada su sayar da ƙuri'unsu, yana mai gargadin cewa hakan zai hana su zaɓen shugabanni nagari tare da jefa makomarsu cikin haɗari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com